Marasa karfi su rage yawan aure-aure — Sarkin Zamfarar Anka

Wasu mata a wajen auren zawarawa a Kano

Gwamnatin Kano ce ta fara aurar da zawarawa da ‘yan mata da nufin rage yawansu da magance matsalar rashin wadatar sayan kayan daki ga iyaye

Mai martaba Sarkin Zamfarar Anka, Alhaji Attahiru Muhd Ahmad ya yi kira ga masu karamin karfi su guji auren mace fiye da d’aya.

Sarkin ya bayyana damuwa kan yadda wasu ke yawan aure ko da ba su da halin rike ‘ya’yan da suka haifa.

Ya kuma soki lamirin al’adar auri-saki, inda ya alakanta ta da karuwar rashin tsaron da ke addabar jihohin arewacin Najeriya.

Sarkin na Anka ya ce babbar matsalar da ake fuskanta ita ce masu karamin karfi sun fi kowa yawan aure-aure alhalin sun san ba su da wadatar kula da iyali.

”Ya kamata ayi wa mata da ‘ya’ya adalci, saboda yawanci za ka ga masu mafi kankantar albashi ke da wannan dabi’a. Za ka ga mai karamin albashin naira 18,000 ya na da matan aure har 3 da kuma wannan albashin ya ke tunkahon kula da su.”

“Akwai mai mace har hudu da ‘ya’ya 30, ta yaya zai iya kula da iyali? idan ka bincika karshen ta ba shi ke kula da su ba”, inji sarkin na Anka.

Ban goyi bayan dabi’ar Auri-saki ba

Haka kuma ya bayyana takaici kan maza masu dabi’ar auri-saki, ”akwai maza masu auri-saki, su auro mace da sun haifi ‘ya’ya daya ko biyu sai ya sake ta idan kuma za ta tafi da ‘ya’yanta ta ke tafiya. Ka ga anan babu batun ya kula da su, ba kuma lallai ace ya na musu aike ba”.

Wasu mata dai sun bayyana ra’ayoyi mabanbanta kan wannan kira, yayin da wasu ke goyon baya, wasu na cewa idan aka hana yawan aure-auren haka ba karamar matsala zai haifar ba sakamakon zawarawa sun yi yawa, wasu mazajensu sun mutu ko an kashe su.

Ba a dai cika jin sarakunan arewa na fitowa bainar jama’a suna jan hakalin mutane, game da yawan aurace-aurace ba, musamman ga wadanda ba su da halin rike iyali da tarbiyyantarwa.

A baya dai, Sarkin Kano Muhammadu Sanusi na bBiyu ya fuskanci suka, lokacin da ya bukaci kafa doka a kan al’amuran auratayya.

More News

Majalisar dokokin jihar Kaduna ta nemi ma’aikatar kudin jihar ta miƙata bayanan bashin da El-Rufai ya ciwo

Majalisar dokokin jihar Kaduna ta nemi ma'aikatar kudi ta jihar da ta miƙa mata cikakken bayani kan basukan  da gwamnatin tsohon gwamnan jihar, Nasiru...

An dakatar da ayyukan kamfanin jiragen sama na Dana Air

Festus Keyamo, ministan harkokin sufurin jiragen sama ya umarci hukumar FAAN dake lura da sufurin jiragen sama a Najeriya ta dakatar da ayyukan kamfanin...

Yahaya Bello Ya Bayyana Dalilan Da Ya Hana Shi Bayyana A Gaban Kotu

Tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello ya ce tsoron kamun  hukumar EFCC dake yaƙi da yiwa tattalin arzikin ƙasa ne ya hana shi bayyana...

Ƴan sanda sun kama mutane biyu dake samarwa ƴan fashin daji makamai a jihar Kaduna

Rundunar ƴan sandan jihar Kaduna ta ce tana tsare da wasu mutane biyu da ake zargi da safarar bindiga a jihar. A wata sanarwa ranar...