Manyan abubuwan da suka faru a wannan makon

Hakkin mallakar hoto
SALIHU TANKO YAKASAI

Tirka-tirkar masarautu a Kano

A wannan makon ne Majalisar zartarwa ta jihar Kano ta sake aikawa da wani sabon kudiri ga majalisar jihar, domin kafa sabbin masarautu.

Wannan na zuwa ne kwanaki kadan bayan wata kotu a Kano ta soke sabbin masarautun da aka kafa a baya, inda ta ce ta yanke wannan hukunci ne saboda an shigar da kudurin bukatar kirkirar masarautun ba bisa ka’ida ba.

Jim kadan bayan hakane Majalisar dokokin jihar ta Kano ta sa hannu kan dokar wadda ta bukaci a kirkiro karin masarautu hudu a jihar.

Bayan majalisar ta saka hannu, ba tare da bata lokaci ba shi ma Gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje ya rattaba hannu a kan dokar.

Dama dai majalisar a baya ta taba amincewa da kudurin, sai dai daga bisani wata babbar kotu a jihar ta rushe ta bisa hujjar rashin cika ka’ida kafin yinta, abin da ya sa gwamnan ya sake gabatar wa majalisar kudurin a karo na biyu.

Hakkin mallakar hoto
NIGERIA PRESIDENCY

Buhari ya kaddamar da jami’ar sufuri a Daura

A ranar Litinin ne Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya ya assasa harsashin gina Jami’ar Sufuri ta farko a kasar.

Za a gina makarantar ne a mahaifar shugaban da ke Daura a jihar Katsina, arewacin Najeriya.

A watan Oktoban 2018 gwamnatin tarayya ta amince da fitar da kudin da za a gina jami’ar, a cewar Hukumar da ke Kula da Jami’o’i ta Najeriya NUC.

Jami’ar Sufurin za ta mayar da hankali ne kan bincike da ci gaban bangaren sufuri a Najeriya.

Wannan makaranta ta gwamnatin tarayya ce, sannan kuma za a bude wata irinta a jihar Ribas da ke kudancin Najeriya, a garinsu Ministan Sufuri Chibuike Amaechi.

Za a kashe dala miliyan 50 wajen gina jami’ar (naira biliyan 18), kamar yadda Amaechi ya fada.

Hakkin mallakar hoto
Ballon d’Or

Messi ya lashe kyautar Ballon d’Or ta 2019

A ranar Litinin ne dan wasan Argentina da kuma Barcelona, Lionel Messi ya lashe kyautar gwarzon dan kwallon kafa ta 2019, wato Ballon d’Or ta 2019.

Messi ya ciyo wa kungiyarsa da kasarsa kwallaye 46 a shekarar 2019.

Dan kwallon ya doke ‘yan wasa kamar su: Virgil van Dijk da Cristiano Ronaldo da Sadio Mane da Mo Salah da Kylian Mbappe da sauransu.

Wannan ne karo na shida da dan wasan ya lashe kyautar.

Messi ya taba lashe kyautar a shekarar 2009 da 2010 da 2011 da 2012 da kuma 2015.

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Buhari ya nada sabon Shugaban Hukumar Alhazai

A ranar Talata ne Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya mika sunan sabon shugaban hukumar alhazai ta Najeriya da mambobinta ga majalisar dattijan kasar.

Majalisar dattawan kasar ta wallafa a shafinta na Twitter cewa ta karanta wata wasika da shugaban kasa ya turo mata kan nada sabon Shugaban Hukumar Alhazai ta Najeriya.

Sunan wanda shugaban kasar ya mika a matsayin wanda yake so a ba shi shugabancin hukumar Zikrullah Olakunle Hassan wanda ya fito ne daga jihar Osun.

Idan har majalisar dattijan ta tabbatar da nadin, to Olakunle ne zai gaji Abdullahi Mukhtar wanda ke kan kujerar tun 2015.

Hakkin mallakar hoto
Sowore

DSS ta sake kama Sowore

A ranar Juma’a ne hukumar tsaro ta farin kaya a Najeriya (DSS) ta sake kama Omoyele Sowore kwana daya bayan ta sake shi.

Wakiliyar BBC ta shaida cewa jami’an DSS sun kama Mista Sowore ne bayan da ya bayyana a gaban kotu a Abuja don ci gaba da sauraren kararsa a ranar Juma’a.

Jami’an sun yi kokarin kama shi tun a cikin kotun, bayan da alkalin da ke sauraren karar ta dage zaman zuwa 11 ga watan Fabrairun 2020 amma sai ya tirje.

Daga nan sai ya fita wajen kotun kuma a nan ne DSS din ta kama Mista Sowore.

An tafi da Mista Sowore a cikin motar lauyansa ne Femi Falana SAN inda jami’in DSS ke tuka motar kuma lauyan nasa ya yi mata rakiya.

More News

EFCC na neman Yahaya Bello ruwa a jallo

Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati (Economic and Financial Crimes Commission) ta bayyana tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello a matsayin...

Mutane da dama sun mutu bayan motar fasinja ta taka bam a Borno

Akalla mutane 16 ne ake fargabar sun mutu yayin da wasu 20 suka jikkata bayan wata motar fasinja da ke kan titin Baga-Kukawa a...

Sojoji Sun Ceto Lydia Simon ĆŠaya Daga Cikin Ćłan Matan Chibok

Dakarun sojan Najeriya dake aiki da rundunar samar da tsaro ta Operation Desert Sanity III sun samu nasarar ceto, Lydia Simon É—aya daga cikin...

Gwamna da ƴansanda sun daƙile yunkurin EFCC na kama Yahaya Bello

A ranar Laraba ne Gwamnan Jihar Kogi, Usman Ododo, ya dakile wani yunkurin da Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati ta...