Alhazan jihar Nasarawa da dama ne suka tsallake rijiya da baya a lokacin da motar da suke ciki tayi hatsari.
Motar maniyyatan ta yi hatsari ne a ranar Laraba a kan hanyarsu ta zuwa Abuja inda za su hau jirgin farko a rana Alhamis.
Hatsarin da ya ritsa da bas mai daukar mutum 18 da suke ciki ne a yankin Kara da ke Karamar Hukumar Keffi ta Jihar Nasarawa.
Da dama daga cikin maniyatan sun jikkata amma ba a samu asarar rayuka ba.
