Connect with us

Hausa

Man Utd ta yi wa Chelsea cin kaca a wasan farko | BBC Hausa

Published

on

Premier

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Kwallon da Anthony Martial ya ci ce ta biyu a jerin kwallaye uku da Man Utd ta ci Chelsea

Kungiyar wasa ta Manchester United ta lallasa daya daga cikin masu adawa da ita wato Chelsea da ci 3-0, a wasan kungiyoyin na farko a kakar gasar Premier ta Ingila.

Yanzu haka Man Utd na da maki uku dai-dai da Manchester City, inda kuma take biye wa Man City a yawan gwala-gwalai.

Dan wasan Manchester United na gaba, Marcus Rashford ne ya fara tona wa ragar Chelsea asiri kafin tafiya hutun rabin lokaci.

Anthony Martial ne ya sake daga ragar Chelsea a minti 65, kafin Marcus Rashford ya sake ganin zaran ragar Chelsea ya tsinka minti guda bayan ta Marshall.

Shi ma sabon dan wasan Man Utd, Daniel James ya wanke kansa ga ‘yan kallo inda ya jefa kwallo ta hudu a ragar Chelsea.

  • Premier: Man City da Tottenham da Liverpool sun fara da kafar dama
  • Yadda aka rufe kasuwar saye da musayar ‘yan wasa ta Ingila

Wannann dai ita ce nasara irinta ta farko da Manchester United ta taba samu a kan Chelsea a Old Trafford tun 1965.

Har wa yau, kwallayen hudu da Man Utd ta jefa a ragar Chelsea a tashin farko sun nuna irin gazawar kocin Chelsea, Frank Lampard a wasansa na farko na Premier League.

Maguire ya rike baya

Masu bibiyar harkar kwallon kafa da ma magoya bayan Manchester United sun ta zura ido domin ganin ko kwalliya za ta biya kudin sabulu dangane da sabon dan wasan baya da kungiyar ta saya a kan tsabar kudi har £80m, Harry Maguire.

Irin wasan da Maguire ya yi wajen kwace kwallo daga hannu dan wasan Chelsea, Tammy Abraham ya bai wa maras da kunya.

Hakan ne ya sa ‘yan kallo magoya bayan kulob dinsa suka yi ta sowa.

Irin nutsuwarsa a lokacin tashin hankali domin kare gidansa a duk lokacin da baraka ta afku ya kayatar da masoya.

Maguire ba ya harba-ta-mati wajen karbar kwallo da rabawa da kuma duba abokan wasan lokacin da ya kamata ya mika kwallo a gare su musamman Paul Pogba.

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Harry Maguire dan wasan da Man Utd ta saya a kan £80m

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Marcus Rashford

Facebook Comments

Hausa

Me ya sa kwanaki hudu babu internet a Iran? | BBC news

Published

on

Iran
Image caption

Rashin internet ya shafi rayuwar ‘yan kasar, musamman matasa

Kasashen duniya sun fara nuna damuwa kan daukewar internet a kasar Iran, a dai-dai lokacin da aka shiga kwanaki hudu da daukewar.

Wannan ya biyo bayan zanga-zangar da ‘yan kasar ke yi kan Karin farshin man fetur da kasha 50, wanda gwamnatin shugaba Hassan Rouhani ta yyana.

A daren Asabar ne internet din ta fara fuskantar tangarda, kafin wayewar garin Lahadi ta dauke baki daya.

Iraniyawa mazauna kasashen ketare sun yi ta wallafwa a shafukan sada zumunta cewa daukewar internet ta raba su da ‘yan uwa da abokan arziki da ke gida lamarin da ya sanya ba su san a halin da suke ciki ba.

  • An kashe masu zanga-zanga 106 a Iran – Kungiyar Amnesty
  • Iran ta ‘samu rijiya mai gangar danyen mai biliyan 53’

Abin ya matukar tayar da hankali a kasar mai al’umma miliyan 80 da yawancin matasa sun dogara da internet dan gudanar da rayuwar yau da kullum ciki har da karatu.

Ba kamar sauran kasashen waje ba kamar Birtaniya da suke da kamfanonin sadarwa da internet daban-daban ba, wanda da wuya su iya daukewa a lokaci guda.

Iran na da kamfanoni biyu kwarara da kuma suke karkashin gwamnati, dan haka ne abin ya yi matukar tasiri.

Wata matashiya Arash Azizah ta wallafa a shafinta na Twitter yadda lamarin ya shafe ta;

”Kamar sauran Iraniyawa, muna da dandalin Whatsapp da zuriyar gidanmu ke amfani da shi, kakarmu a duk asubahin Allah ta na tura mana sakon fatan alkhairi da kariya daga dukkan abin ki, amma wannan matsala da aka samu ta hana mu yin hakan.”

Facebook Comments
Continue Reading

Hausa

An damke tsohon minista Adoke a Dubai

Published

on

Adoke

Hukumar ‘yan sandan kasa da kasa watau Interpol ta damke tsohon ministan shari’ar Najeriya bisa zargi sa da hannu a wata badakalar cin hanci kan danyen mai na fiye da dala biliyan daya.

Lauyan Mr Mohammed Bello Adoke ya tabbatar da tsare tsohon ministan a Dubai, amma ya ce bisa wani sammaci ne da lokacinsa ya wuce.

A baya Mr Adoke ya ce bai ci komai ba game da wata yarjejeniyar sayar da wata rijiyar mai a shekara ta 2011.

A cikin watan Afrilu ne hukumar yaki da rashawa a Najeriya – EFCC ta ba da sammacin kama shi tare da tsohon ministan man kasar, Dan Etete da kuma wani manaja a kamfanin mai na Italiya mai suna Eni.

Lamarin ya janyo shari’a mai tsawo tsakanin gwamnatin Najeriya da wasu kusoshi a kamfanonin mai na Eni da kuma Shell.

Sai dai duk kamfanonin biyu sun musanta aikata ba dai-dai ba.

Facebook Comments
Continue Reading

Arewa

Mece ce Fassarar “Baƙonka Annabinka” Zuwa Turanci?

Published

on

Wani ya yi tambaya game da ma’ana tare da fassarar wannan karin magana da Hausawa ke cewa “Baƙonka annabinka.” To sai dai ba dole ba ne a samu lafazi a Turanci wanda kai-tsaye zai dace da shi domin harsunan biyu suna da matuƙar bambanci dangane da al’adu da tunaninsu – kamar yadda masana harshe suka tabbatar cewa ba a raba harshe da al’ada da tunanin mutane masu harshen.

Duk da haka, a fannin ilimin fassara, akwai wasu dabarbaru da ake amfani da su wajen fassara lafazi da ba a samunsa a harshen ƙarba (wato target language a Turance). Saboda haka, mai fassara zai yi iya ƙoƙarinsa wajen ganin cewa ya yi lafiyayyar fassara wacce ba za ta kautar da ma’anar lafazin da yake son fassarawa ba.

Duba da wannan bayani, ni a tawa fahimtar, za a iya fassara lafazin “Baƙonka annabinka” zuwa Turanci ya koma “Your visitor deserves your kindness.”

Muhammadu Sabiu

Facebook Comments
Continue Reading

Trending

© Copyright 2019 - AREWANG Media Limited