Man Utd da City: ‘Yan Liverpool sun jingine adawa

'Yan Liverpool sun zama magoya bayan Manchester United na rana daya

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Dimbin magoya bayan Liverpool sun ce a karon farko za su goyi bayan Manchester United a wasan da za ta fafata da Manchester City a gasar Premier.

Wasan zai ja hankali da ake ganin zai tantance wanda zai lashe kofin Premier na bana tsakanin Liverpool da Manchester City.

Tazarar maki biyu Liverpool ta ba Manchester City a teburin Premier, yayin da ya rage wasanni uku a kammala gasar.

Wasan dai kwante ne ga Manchester City wanda zai ba Guardiola damar darewa tebur idan ya doke Manchester United a Old Trafford.

Yawancin ‘yan wasa da magoya bayan Liverpool sun ce wannan ne karon farko da za su goyi bayan Manchester United a wani wasa.

Suna ganin United din ce za ta ba su nasarar lashe kofin Premier na bana idan har ta doke Manchester City ko ta rike ta kunnen doki.

Dan wasan Liverpool James Milner ya ce wannan ne karon farko a rayuwarsa da zai goyi bayan babbar abokiyar gaba Manchester United.

Sai dai dan wasan ya ce ba zai iya kallon wasan ba, yana mai cewa bata lokaci ne.

Wasu na ganin ya rage ga Manchester United ga wanda take son ya lashe kofin Premier na bana tsakanin manyan abokan gabarta guda biyu Liverpool da Manchester City.

Sai dai wasu na ganin ‘Yan Manchester United ba za su taba son Liverpool ta lashe kofin Premier ba saboda girman gabar da ke tsakanin kungiyoyin biyu.

Wasu magoya bayan Manchester United sun ce sun fi kaunar Manchester City ta lashe kofin da ace Liverpool ce ta lashe saboda girman gabar da ke tsakaninsu.

Wani dan Liverpool kuma ya ce ba zai taba goyon bayan Manchester United ba duk da cewa yana matukar son City ta yi bari a Old Trafford.

Ana dai amfani da karawar da Manchester United za ta yi da Manchester City domin shammatar magoya bayan Liverpool musamman gabar da ke tsakaninsu da Manchester United.

More News

EFCC na neman Yahaya Bello ruwa a jallo

Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati (Economic and Financial Crimes Commission) ta bayyana tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello a matsayin...

Mutane da dama sun mutu bayan motar fasinja ta taka bam a Borno

Akalla mutane 16 ne ake fargabar sun mutu yayin da wasu 20 suka jikkata bayan wata motar fasinja da ke kan titin Baga-Kukawa a...

Sojoji Sun Ceto Lydia Simon Ɗaya Daga Cikin Ƴan Matan Chibok

Dakarun sojan Najeriya dake aiki da rundunar samar da tsaro ta Operation Desert Sanity III sun samu nasarar ceto, Lydia Simon ɗaya daga cikin...

Gwamna da ƴansanda sun daƙile yunkurin EFCC na kama Yahaya Bello

A ranar Laraba ne Gwamnan Jihar Kogi, Usman Ododo, ya dakile wani yunkurin da Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati ta...