Malamai Sun Amince Da Dakatar Da Sallar Juma’a A Kano – AREWA News

Tawagar manyan Malamai a jihar Kano sun amince da dakatar da sallar juma’a a daukacin masallatan jihar, a yayin da dokar hana fita da gwamnati ta saka ke fara aiki a yau Alhamis.

Malaman dai sun gudanar da taron nasu ne a Africa House da ke fadar gwamnatin Kano ranar Alhamis, karkashin kwamitin kar ta
kwana na cutar korona da Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya kafa.

Idan an jima ne dokar hana fita da gwamnatin jihar ta kafa za ta fara aiki, wadda za a shafe tsawon mako guda. Shawararin malaman dai na zuwa ne bayan da hukumomi a jihar Kano
suka sanar da mutuwar wani mutum mai dauke da cutar korona a jihar, yayin da adadin wadanda suka kamu da cutar ya kai mutum 21.

Malaman sun yi nazarin harkokin rayuwar al’umma ne wadanda ke da nasaba da taron
jama’a da nufin bayar da fatawa, inda suka amince da dakatar da Sallar Juma’a a masallatan jihar da kuma tarukan da ake yi da suka shafi karatu a lokacin watan Ramadan, don hana yaduwar cutar korona a tsakanin al’umma.

Dr. Ibrahim Mu’azzam mai Bushira shi ne sakataren karamin kwamitin malamai da kwamitin kar ta kwana na coronavirus ya kafa, wanda ya ce malaman sun amince da a dakatar da gabatar da Sallar Juma’a don gudun kada wani da yake dauke da cutar ya yada ta a tsakanin al’umma.

More News

MTN yana ƙoƙarin ƙara kuɗin kati da data a Najeriya

Katafaren kamfanin sadarwa na MTN na kokarin kara kudin katin waya da na data a Najeriya. Kamfanin sadarwa mafi girma a nahiyar Afirka ya ba...

Gwamnatin Kano Ta Rage ₦500,000 A Kuɗin Aikin Hajjin Bana

Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya sanar da yiwa maniyatan Aikin Hajji da suka fito daga jihar kyautar ₦500,000 domin su cika kuɗin...

Ƴan bindiga sun sace wani limami a jihar Kogi

Ƴan bindiga sun yi garkuwa da Quasim Musa babban limamin garin Iyara dake ƙaramar hukumar Ijumu ta jihar Kogi. Lamarin ya faru ne a ranar...

Delta: An dawo da gawarwakin sojojin da aka kashe Abuja don yi musu jana’iza

Gawarwakin sojojin da aka kashe a jihar Delta kwanan nan sun isa maƙabartar sojoji ta kasa da ke Abuja. Gawarwakin sun iso ne da misalin...