Majalisar dokokin jihar Kaduna ta nemi ma’aikatar kudin jihar ta miƙata bayanan bashin da El-Rufai ya ciwo

Majalisar dokokin jihar Kaduna ta nemi ma’aikatar kudi ta jihar da ta miƙa mata cikakken bayani kan basukan  da gwamnatin tsohon gwamnan jihar, Nasiru El-Rufai ta ciwo.

Buƙatar da majalisar ta miƙa na zuwa ne dai-dai lokacin da majalisar  ke cigaba da bincike kan sha’anin kuɗin jihar a zamanin mulkin na El-Rufai.

El-Rufai ya mulki jihar daga shekarar 2015 da 2023.

A ranar Talatar da ta wuce majalisar ta kafa kwamitin da zai binciki gwamnatin El-Rufai.

Kwamitin mai wakilai 13 an ɗora masa alhakin binciken basussuka, tallafin kuɗaɗe da kuma ayyukan da aka aiwatar daga shekarar 2015 ya zuwa 2023.

A wata wasiƙa mai ɗauke da kwanan watan 22 ga watan Afrilu da akawun majalisar Sakinatu Idris ta sawa hannu kuma aka  aikewa kwamishinan kuɗin jihar ta nemi bayanai da ya shafi biyan ƴan kwangilar kuɗin kwangiloli a zamanin mulkin El-Rufai.

A ranar 30 ga watan Maris ne gwamnan jihar,Mallam Uba Sani ya ce gwamnatinsa ta gaji bashin dala miliyan $587 bashin biyan ayyukan ƴan kwangila 115.

More from this stream

Recomended