Majalisar Dokoki Ta Takwas Ta Yi Zaman Ta Na Karshe

VOA Hausa

Jiya Alhamis ne Majalisar Dokokin Najeriya ta kammala zaman ta, inda ta yi bikin bankwana da ya kwashi sa’o’i bakwai wanda ya nuna cewa an zo karshen zaman Majalisar bayan ta kwashi shekaru 4 ta na yin dokoki da suka shafi rayuwar al’umma ko akasin haka.

Daya bayan daya ne ‘ya ‘yan Majalisar Dokokin Najeriya suka rika tashi suna yi wa juna bankwana bayan sun kwashi shekaru hudu suna yi wa kasa dokoki da suka shafi rayuwar al’umma.

Majalisar Dattawa ta ce ta yi aiki akan dokoki dar shida (600) wanda a ciki sun amince da dari uku da goma sha tara 319, sanan a Majalisar Wakilai kuma, sun yi aiki a kan dokoki 1,588 a ciki sun amince da 382. Amma akwai dokoki 65 wanda Shugaba Mohammadu Buhari ya amince da kansa.

A lokacin da yake jawabinsa Shugaban Majalisar Dattawa ya ce ba a taba samun Majalisar da ta yi wa ‘kasa aiki kamar Majalisa ta 8 ba domin ita ce tafi kowacce yin dokoki.

A bangaren Majalisar Wakilai kuma, an yi aiki akan dokoki 1,588 amma aka amince da dokoki 382. Dukkan Majalisun biyu sun sami korafe-korafe da dama, amma wajen 132 ne a ka samu nasarar magance su.

Shi kuwa, Akawun Majalisar Kasa Mohammed Sani Omolori ya ce ya samu takardar umurnin rufe Majalisar daga wurin Shugaba Mohammadu Buhari saboda haka za a rufe Majalisar ranar 8 ga wanan wata. Sannan ranar 11 ga wanan wata za rantsar da sabuwar Majalisar Dokoki ta tara.

Sanata Sahabi Ya’u daga jihar Zamfara ya ce zai ba Majalisa ta tara gagarumin gudumawa da zai taimaka wajen yaye matsalolin da kasa ta ke fuskanta.

Shi ma sabon dan Mjalisar Wakilai daga Jihar Zamfara suleiman Abubakar Gumi ya ce zai tabbatar cewa an samu hadin kai a Majalisar domin Kasa ta ci gaba.

Tsofaffin yan Majalisar masu barin gado sun bada shawarar sa ido a aiyukan bangaren zantasawa domin a samu nasarar yaki da cin hanci da rashawa.

More News

Majalisar dokokin jihar Kaduna ta nemi ma’aikatar kudin jihar ta miÆ™ata bayanan bashin da El-Rufai ya ciwo

Majalisar dokokin jihar Kaduna ta nemi ma'aikatar kudi ta jihar da ta miƙa mata cikakken bayani kan basukan  da gwamnatin tsohon gwamnan jihar, Nasiru...

An dakatar da ayyukan kamfanin jiragen sama na Dana Air

Festus Keyamo, ministan harkokin sufurin jiragen sama ya umarci hukumar FAAN dake lura da sufurin jiragen sama a Najeriya ta dakatar da ayyukan kamfanin...

Yahaya Bello Ya Bayyana Dalilan Da Ya Hana Shi Bayyana A Gaban Kotu

Tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello ya ce tsoron kamun  hukumar EFCC dake yaÆ™i da yiwa tattalin arzikin Æ™asa ne ya hana shi bayyana...

Ƴan sanda sun kama mutane biyu dake samarwa ƴan fashin daji makamai a jihar Kaduna

Rundunar Æ´an sandan jihar Kaduna ta ce tana tsare da wasu mutane biyu da ake zargi da safarar bindiga a jihar. A wata sanarwa ranar...