Hajiya Dada, mahaifiyar tsohon shugaban Najeriya, marigayi Umaru Musa Yar’adua, ta rasu.
Rahotanni sun bayyana cewa ta rasu ne a asibitin koyarwa na gwamnatin tarayya da ke Katsina a ranar Litinin bayan gajeriyar rashin lafiya.
Ta rasu tana da shekaru 102.
Dada ta kasance mahaifiyar marigayi Shehu Musa Yar’adua da kuma Sanata Abdulaziz Musa Yar’adua, shugaban kwamitin majalisar dattawa a kan sojoji a yanzu.
Nan gaba ‘yan’uwanta za su bayyana shirin binne ta.Â
Umaru Musa ‘Yar’adua ya yi shugaban kasar Najeriya daga shekarar 2007 har zuwa rasuwarsa a watan Mayun 2010.
Ya taba rike mukamin gwamnan jihar Katsina daga 1999 zuwa 2007.