Lionel Messi zai lashe Ballon d’Or na bakwai jumulla

Kyaftin Lionel Messi ya lashe Copa America da Argentina da hakan ya kawo karshen shekara 28 da kasar ta kasa daukar babban kofi a fannin tamaula.

Ranar Asabar Argentina ta doke Brazil mai masaukin baki ta kuma lashe Copa America, karon farko da dan wasan Barcelona ya ci kofi a tawagar kasarsa.

Wannan bajintar da Messi ya yi ya kawo karshen masu masa gorin kasa daukar kofi a Agentina, kuma hakan ake ganin watakila ya lashe Ballon d’Or na bakwai jumulla.

Duk wanda ya lashe Copa America ko European Championship ko kuma kofin duniya, sannan ya taka rawar gani a kungiyarsa, ana masa tsammanin zai iya lashe babbar kyautar Fifa a shekarar.

Dalilin da wasu ke hangen Messi ne zai karbi kyautar gwarzon kwallon kafa na duniya sun hada da cewar a wasa 47 da ya yi a bana ya ci kwallo 38 ya bayar da 14 aka zura a raga.

Haka kuma kyaftin din na Barcelona ya karbi kyautar fitatcen dan wasa a fafatawa 26 a shekarar 2021 wato best player award.

Messi shine ya lashe takalmin zinare a matakin wanda ke kan gaba a cin kwallaye a La Liga, kuma shine na daya a zazzaga kwallaye a Copa America mai hudu, sannan ya bayar da biyar aka zura a raga.

Hakan na nufin Messi mai Ballon d’Or shida a tarihi yana da hannu a kwallo 12 da Argentina ta zura a raga a Copa America.

Bayan da ya lashe Copa America a Brazil, tun kafin gasar Messi ya dauki Copa del Rey a Barcelona a kakar da aka kammala.

Messi ya fara cin kyautar Ballon d’Or a 2009 daga nan ya sake dauka a, 2010 da 2011 da 2012 da 2015 da kuma 2019.

Wadanne ‘yan wasa ne zai iya takara da su?

Idan aka yi maganar Kylian Mbappe, bai lashe Ligue 1 ko kuma Champions League ba, haka Cristiano Ronaldo bai dauki Serie A ba, balle kofin nahiyar Turai da aka karbe daga hannunsu.

Robert Lewandowski ya karya tarihin cin kwallaye a Bundesliga ta Jamus, amma bai taka rawar gani a gasar Euro 2020 ba.

Wadanda za su zama barazana ga Messi a kyautar ta Ballon d’Or sun hada da Giorgio Chiellini da kuma Leonardo Bonucci, wadanda suka dauki Euro 2020.

Haka kuma da dan kwallon Chelsea, N’Golo Kante da kuma Mason Mount wadanda suka lashe Champions League suka kuma taka rawar gani.

More News

EFCC na neman Yahaya Bello ruwa a jallo

Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati (Economic and Financial Crimes Commission) ta bayyana tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello a matsayin...

Mutane da dama sun mutu bayan motar fasinja ta taka bam a Borno

Akalla mutane 16 ne ake fargabar sun mutu yayin da wasu 20 suka jikkata bayan wata motar fasinja da ke kan titin Baga-Kukawa a...

Sojoji Sun Ceto Lydia Simon ĆŠaya Daga Cikin Ćłan Matan Chibok

Dakarun sojan Najeriya dake aiki da rundunar samar da tsaro ta Operation Desert Sanity III sun samu nasarar ceto, Lydia Simon É—aya daga cikin...

Gwamna da ƴansanda sun daƙile yunkurin EFCC na kama Yahaya Bello

A ranar Laraba ne Gwamnan Jihar Kogi, Usman Ododo, ya dakile wani yunkurin da Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati ta...