Limaman Saudiyya za su yi jagorancin sallar asham a kasashe 35

sallah
Hakkin mallakar hoto
Getty Images
Image caption

Shirin wani kokari na masarautar don nuna kulawa da tallafawa dukkan musulmai a duk inda suke

Ministan harkokin addinin musulunci na Saudiyya Abdullatif Al-Asheikh, ya amince da tura tawagar limamai 70 don jagorantar sallolin Tarawih (asham) da Tahajjud a kasashe 35 na duniya a lokacin azumin Ramadan.

Dama dai ma’aikatar ta saba aika limamai wasu kasashen lokacin azumi don jagorantar sallolin da kuma wayar wa da musulmai kai dangane da abun da ya shafi addini.

Jaridar Saudi Gazeete ta ruwaito ministan yana cewa hakan wani bangare ne na kokarin masarautar don nuna kulawa da tallafawa dukkan musulmai a duk inda suke.

Ya ce limaman za su dora al’ummar musulmai kan turba ta gaskiya, su bayyana musu ainihin sakon musulunci na gaskiya su kuma wayar musu da kai kan duk abun da ya shafi rayuwar musulmi.

“An zabi malaman ne daga kwalejojin Shari’ah. Dukkansu mahaddatan Al-Kur’ani mai girma ne kuma masana sosai a addinin,” in ji shi.

“Wadannan matasan malamai kwararrun masu wa’azi ne wadanda za su iya yi wa Musulmai bayanin addinin Musulunci sosai, kuma za su iya karanto Al-Kur’ani da ka,” in ji shi.

Al-Asheikh ya ce masallatan kan cika makil da masu ibadah a lokacin azumi don haka babbar dama ce ga limaman su tafiyar da lokacinsu wajen amfanar mutane da wayar musu da kai.

Hakkin mallakar hoto
Saudi Gazette
Image caption

Ministan yayin da yake ganawa da malaman

“Limaman za su isar da sakon Musulunci da kuma karfafa danganta tsakanin Masarautar Saudiyya da kasashen da aka tura malaman,” a cewarsa.

A ranar Litinin ne ministan ya gana da limaman ya kuma umarce su su zamo wakila nagari ga kasarsu.

Ma’aikatar ta shirya musu wani taron karawa juna sani don kara wayar da kansu kan hanyoyin da ya kamata su bi wajen yada sakon musulunci a kasashen waje.

More News

MTN yana ƙoƙarin ƙara kuɗin kati da data a Najeriya

Katafaren kamfanin sadarwa na MTN na kokarin kara kudin katin waya da na data a Najeriya. Kamfanin sadarwa mafi girma a nahiyar Afirka ya ba...

Gwamnatin Kano Ta Rage ₦500,000 A Kuɗin Aikin Hajjin Bana

Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya sanar da yiwa maniyatan Aikin Hajji da suka fito daga jihar kyautar ₦500,000 domin su cika kuɗin...

Ƴan bindiga sun sace wani limami a jihar Kogi

Ƴan bindiga sun yi garkuwa da Quasim Musa babban limamin garin Iyara dake ƙaramar hukumar Ijumu ta jihar Kogi. Lamarin ya faru ne a ranar...

Delta: An dawo da gawarwakin sojojin da aka kashe Abuja don yi musu jana’iza

Gawarwakin sojojin da aka kashe a jihar Delta kwanan nan sun isa maƙabartar sojoji ta kasa da ke Abuja. Gawarwakin sun iso ne da misalin...