Kwankwaso ya faɗi dalilin da ya sa bai halarci babban taron Kungiyar Lauyoyin Najeriya ba.

Dan takarar shugaban kasa karkashin jam’iyyar NNPP a Najeriya Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya ce bai amsa gayyatar da kungiyar lauyoyin Najeriya ta yi masa ba ne saboda wasu muhimman ayyuka da suka sha gabansa.

Cikin wata wasika da ya rubutawa kungiyar lauyoyin ta NBA, wacce kakakinsa Abdulmumin Jibril ya wallafa a shafinsa na Facebook, Kwankwaso, ya bai wa kungiyar hakuri bisa rashin samun damar halartar taron.

“Ina so na bayyana cewa na samu wasikar gayyatarku, mai dauke da maudi’in da ya gabata, ina kuma so na sanar da ku cewa ba zan samu damar halartar wannan taro mai muhimmanci ba, saboda wasu muhimman abubuwa da ke gabana da suka shafi kasa.” Kwankwaso ya ce cikin wasikar.

Cikin wasikar, Kwankwaso har ila yau ya ce, abokin takararsa Bishop Isaac Idahosa ya fita kasar waje, “amma da na turo shi don ya wakilce ni.”

A ranar Litinin kungiyar ta NBA ta bude babban taronta na kasa a karo na 62 a jihar Legas da ke kudu maso yammacin Najeriya.

Taron ya samu halartar dan takarar shugaban kasa karkashin jam’iyyar PDP Atiku Abubakar da dan takarar jam’iyyar LP, Peter Obi.

Kamar Kwankwaso, shi ma dan takarar jam’iyya mai mulki ta APC, Bola Ahmed Tinubu, bai samu halatar taron ba, amma ya tura abokin takararsa Kashim Shettima don ya wakilce shi.

Ire-iren wadannan taruka kan gayyaci ‘yan takarar mukamin shugaban kasa don su kyankyasawa jama’a manufofinsu kan yadda za su tunkari matsalolin kasa.

More News

EFCC na neman Yahaya Bello ruwa a jallo

Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati (Economic and Financial Crimes Commission) ta bayyana tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello a matsayin...

Mutane da dama sun mutu bayan motar fasinja ta taka bam a Borno

Akalla mutane 16 ne ake fargabar sun mutu yayin da wasu 20 suka jikkata bayan wata motar fasinja da ke kan titin Baga-Kukawa a...

Sojoji Sun Ceto Lydia Simon Ɗaya Daga Cikin Ƴan Matan Chibok

Dakarun sojan Najeriya dake aiki da rundunar samar da tsaro ta Operation Desert Sanity III sun samu nasarar ceto, Lydia Simon ɗaya daga cikin...

Gwamna da ƴansanda sun daƙile yunkurin EFCC na kama Yahaya Bello

A ranar Laraba ne Gwamnan Jihar Kogi, Usman Ododo, ya dakile wani yunkurin da Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati ta...