Kungiyar Likitoci ta NARD Ta Dakatar Da Zanga-Zangar Da Ta Shirya Yi

Kungiyar Likitoci Masu Neman Kwarewa ta NARD ta dakatar da zanga-zangar da suka shirya yi a fadin Najeriya ranar 9 ga watan Agusta.

Wakilan gwamnatin tarayya sun gana da yan kungiyar likitocin a ranar Talata kan shirunsu na fara yajin aikin da kuma zanga-zangar.

Emeka Orji, shugaban kungiyar ya ce abun da aka cimma a wurin ganawar shi zai tabbatar ko za ayi zanga-zangar.

Orji ya fadawa jaridar The Cable cewa an dakatar da yin zanga-zangar kuma za su sake tsayar da matsaya cikin awanni 72.

Kungiyar ta yi hakan ne bayan ganawar da tayi da Godswill Akpabio shugaban majalisar dattawa da kuma wasu daga cikin jagororin majalisar.

More from this stream

Recomended