Kungiyar Kadiriyya ta haura ‘shekara dari tara da kafuwa’ | BBC Hausa

A yayin wata hira da BBC, shugaban kungiyar Kadariyya na Afrika Sheikh Karibullah Sheikh Nasir Kabara, ya ce kungiyar ta samo asali ne tun zamanin Sheikh Abdulkadir Jilani wanda ya assasa ta shekaru da dama.

Ya ce ana gudanar da bikin Maukibi domin tunawa da Sheikh Abdulkadir Jailani da kuma tunatar da jama’a kan hidimarsa ga addinin Islama.

Ya kuma ce Sufaye na dariku ne suka yi sanadin shigowar musulunci a yankin nahiyar Afrika. Kuma a cewarsa “Sheikh Usman Danfodio, ya yi jihadinsa da tutar Kadiriyya.”

Kungiyar dai na daya daga cikin kungiyoyin addinin musulunci da suka fi tasiri a kasashen yammacin Afrika, ko da yake tana da dumbin mabiya a sauran kasashen duniya daban-daban.

More News

Gwamnatin Tarayya Za Ta Fara Rabon Gidaje 8925

Gwamnatin tarayya ta ce ta fara raba gidaje 8925  ga mutanen da suka nema kuma suka cancanci a basu a faɗin ƙasa baki ɗaya...

Ƴan Bindiga A Zamfara Sun Kashe Sakataren Jam’iyar PDP

Wasu ƴan bindiga da ba a san ko suwaye ba sun kashe, Musa Ille  sakataren jam'iyar PDP na ƙaramar hukumar Tsafe a jihar Zamfara. Zagazola...

Hukumar NDLEA ta lalata sama da tan 300 na miyagun kwayoyi da aka kama a Legas da Ogun

Hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa NDLEA ta yi nasarar lalata kilogiram 304,436 da lita 40,042 na haramtattun abubuwa da...

APC ta dakatar da Ganduje a matakin gunduma

Mambobin jam'iyyar APC a mazabar da ke Karamar Hukumar Dawakin Tofa a Jihar Kano sun dakatar da Shugaban Jam’iyyar APC na kasa Abdullahi Ganduje. ...