Kun san garin da babu masallaci sai na haya?

Habasha

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Mata mabiya addinin Kirista a birnin Aksum mai tsarki na kasar Habasha

Mabiya addinin Kirista Kibdawa a kasar Habasha suna kallon birnin Askum da mai tsarki, saboda nan ce mahaifar sarauniya Sheba wadda aka amabata a cikin littafin Injila, da kuma akwatin gwal da Kibdawa sukai amanna ya kunshi wasu muhimman abubuwa na ubangiji.

Sun yi amanna akwatin ya kunshi abubuwa guda 10 masu muhimmanci wanda suka ce Allah ya bai wa Annabi Musa AS wanda ya ke cike da matakan tsaro.

Wasu kungiyoyin Musulmai na gangamin ganin an ba su damar gina masallaci a birnin, batun da shugabannin Kirista suka yi watsi da shi tare da shan alwashin da su ga wannan rana da za a gina masallacin gara ace sun bar duniya.

Wani babban limamin Kibdawa Godefa Merha ya ce suna kallon birnin Askum mai tsarki, tamkar yadda Musulmai ke kallon birnin Makka.

Ya kara da cewa ”kamar yadda aka haramta gina Coci a birnin Makka da Madina haka mu ma muka haramta gina masallaci a Askum mai tsarki”.

“Aksum waje ne mai cikakken tsarki, ba za mu amince a gurbata mana shi ba”, in ji Mr Godefa, wanda shi ne mataimakin majami’ar Our Lady Mary of Zion da ke birnin.

Shekara da shekaru kenan da Kireistoci Kibdawan suka ki amincewa da gina masallatai a birnin, amma a yanzu lamarin ya fi kamari saboda kiraye-kirayen sun karu.

Gangamin da ya ke kara fadada an yi masa taken ”Adalci ga Musulman Aksum”, da kuma bukatar su ma a ji muryarsu su na kiran sallah cikin manyan lasifa.

Mabiya addinnin Musulunci da Kirista sun yi amanna da cewa Musulmai ne suka same su a masarautar Aksum, wanda daya ce daga cikin manyan masarautu a duniya.

Musulmai sun isa jim kadan bayan bayyanar addinin Musulunci a shekarar 600AD a matsayin ‘yan cirani da suka gujewa kisan gillar da kafiran Makka ke musu a wancan lokacin.

Kuma sun karbe su hannu biyu-biyu, tare da ba su damar gudanar da addinin Musulunci a bainar jama’a wanda nan ne wuri na farko da ya aminta da hakan a wajen yankin Larabawa.

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Wannan wata kasuwa ce da ke birnin Aksum da yawancin Musulmai ke zaune

Kashi 10 cikin 100 na mutum 73,000 na birnin mabiya addinin musulunci ne, yayin da Kiristoci Kibdawa suka dauki kashi 85, sai kuma kashi 5 sauran mabiya addinin Kirista.

An tilastawa Musulmai yin sallah a waje

Wani mazaunin birnin mai suna Abdu Mohammed Ali, mai shekara 40, ya ce shekara da shekaru zuriyar gidansu na karbar hayar gidaje ne daga Kirista dan samar da masallacin da za su yi sallah da sauran ibada.

Ya kara da cewa ”muna da masallatai 13 da dukkansu haya muke biya. A duk ranakun juma’a idan mukai kiran sallah ta amfani da lasifika, sai Kiristoci su ce wai mun raina Nana Maryam mahaifiyar Annabi Isa AS”.

Shi ma wani likitan gargajiya Aziz Mohammed, da yake zaune a birnin sama da shekara 20, ya ce a wasu lokutan akan tilastawa Musulmai yin sallah a bainar jama’a ba cikin masallaci ba.

“Mabiya addinin Musulumci da Kirista na zaune a wajen nan shekara da shekaru ba tare da anji kansu ba, kuma ba a taba hana Musulmai yin sallah ba. Amma a yanzu lamarin ya sauya, yawancinmu akan hanya muke sallah don haka muke bukatar a ba mu damar gina masallaci na dindindin,” inji Aziz.

Ya kamata mu zauna lafiya

Sama da shekara 50 da suka gabata an taba samun matsala irin wannan a lokacin mulkin Haile Selassie.

Daya daga cikin iyalan masarautar ya sanya Musulmai suka gina masallaci nisan kilomita 15 daga garin Wukiro-Maray.

Image caption

Musulmai mazauna garin Wukiro-Maray suna da damar zabar yin sallah cikin masallatai biyar da suke da shi

A lokacin da BBC ta kai ziyara garin, wanda mabiya addinin Kirista suka fi rinjaye, mun gana da wata mace mai suna Keriya Mesud wadda ke dafawa Musulmai da ke ibada abinci.

Ta nuna mana masallatai biyar da suke Wukiro-Maray inda nan ne kadai suke da sukunin gudanar da ibada. Ta ce duk da suna bukatar masallaci a birnin Aksum amma babu yadda za su yi, tun da suna son zaman lafiya dole su hakura.

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Mista Godefa ya yi amanna sauran kabilun da ke yankin na zaman lafiya, sannan babban amininsa Musulmi ne komai tare suke yi tun daga zuwa gidan biki, radin suna ko jana’iza.

Sannan ana ganin mabiya addinin Musulunci da ke sauran biranen kasar Habasha suna taimakawa gangamin da ake yi a yanzu na gina masallaci a Aksum.

Sai dai ya yi rantsuwa kan Kibdawa ba za su taba karya alkawarin da suka yi wa magabatansu ba kan cewa ba za su aminci a gurbata birnin ba, wanda kuma suke ganin gina masallaci tamkar gurbata addininsu ne.

Mista Godefa ya ce “Matukar muka bari aka gina masallaci a birni mai tsarki mutuwa za su yi, saboda ba a taba yin hakan ba don haka ba za mu amince ayi ba. Ya zama dole mu ci gaba da mutunta abin da muka gada daga iyaye da kakanninmu na shekaru aru-aru”.

Kiristoci Kibdawa sun yi amanna da cewa bai kamata aji komai a birnin baya ga wakokin yabo da bege da addu’o’in addininsu da aka saba ji tun bayan gina Aksum shekara 7,500 da suka gabata.

Shi ma wani mai wa’azin Kirista Amsale Sibuh ya bayyana cewa “Duk addinin da bai amince da haihuwar Is al-Masiyu ba, bai amince da wankan tsarki na mabiya Kirista ba, da mutuwa, da tashin Annabi Isa, da cetonsa ba, da sake dawowarsa, to ba za mu amince da shi ba.

Idan muka bari aka taka addininmu lallai za mu tabe, mu kuma ba ma fatan hakan”.

Image caption

Limamin Kirista a birnin Askum Amsale Sibuh

Jami’an gwamnati sun ki cewa uffan kan batun gina masallacin, inda suka ce ba za su tsoma baki kan abin da ya shafi mabiya addinan biyu ba saboda sun dade suna zaune tare cikin kwanciyar hankali da zaman lafiya don haka su sasanta kansu.

Kiristoci Kibdawa na ganin gwamnatin kasar Habasha da Firaminista Abiy Ahmed ke jagoranta, wanda mahaifinsa Musulmi ne, mahaifiyarsa kuma Kirista, zai shiga tsakani da fatan zai kare martabar birnin Aksum mai tsarki daga tabewa.

Ya yin da a bangare guda Musulmai ke ganin za su kara matsa kaimi don samun biyan bukata.

Haka kuma wata kungiyar Musulmai a kasar tana shirin gudanar da babban taro domin tattauna batun, suna masu cewa mabiya addinan biyu ya kamata su amince da hakan, suna fatan ganin Kiristoci Kibdawa sun taimaka wajen gina masallaci.

More News

EFCC na neman Yahaya Bello ruwa a jallo

Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati (Economic and Financial Crimes Commission) ta bayyana tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello a matsayin...

Mutane da dama sun mutu bayan motar fasinja ta taka bam a Borno

Akalla mutane 16 ne ake fargabar sun mutu yayin da wasu 20 suka jikkata bayan wata motar fasinja da ke kan titin Baga-Kukawa a...

Sojoji Sun Ceto Lydia Simon ĆŠaya Daga Cikin Ćłan Matan Chibok

Dakarun sojan Najeriya dake aiki da rundunar samar da tsaro ta Operation Desert Sanity III sun samu nasarar ceto, Lydia Simon É—aya daga cikin...

Gwamna da ƴansanda sun daƙile yunkurin EFCC na kama Yahaya Bello

A ranar Laraba ne Gwamnan Jihar Kogi, Usman Ododo, ya dakile wani yunkurin da Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati ta...