Kun san fadi tashi da Najeriya ta yi a fannin wasanni tun daga 1960? | BBC Hausa

Tun lokacin da Nigeria ta samu ‘yancin kai a shekarar 1960 kawo yanzu ta taka rawar gani a fannin wasanni da dama, ta kuma ci karo da cikas iri-iri.

Najeria ta haskaka a wasanni da dama da suka hada da kwallon kafa da damben boksin da kwallon kwando da na tennis da wasannin nakasassu a nahiyar Afirka da duniya tun kafin samun ‘yancin kai a 1960.

Hakan ya sa ta yi kawaye da abokan hamayya da suke gwabzawa a duk lokacin da wasa ya hada su, sannan ta samar da zakakuren ‘yan wasa da suka yi suna kuma suka wakilce ta a fanni da dama da wasunsu ma suka samu aikin yi.

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Kwallon kafa – Tawagar Najeriya da ake kira Super Eagles ta dauki kofin nahiyar Afirka uku kawo yanzu, ta kuma je wasannin karo da dama.

Super Eagles ta ci kofin nahiyar Afirka a karon farko a 1980 sannan ta ci na biyu a 1994 da kuma 2013 da ta lashe na uku jumulla.

A gasar kofin nahiyar Afirka sau 18 Najeriya ta halarci wasannin.

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Tun farko ana kiran tawagar ta Najeriya da sunan Green Eagles wadda ta fara zuwa gasar nahiyar Afirka a 1963 shekara uku da samun ‘yancin kai.

Super Eagles ta saka kaimi a wasanninta inda ta je gasar cin kofin duniya karo shida, bayan da ta fara halarta a 1998, kuma wanda ta fi taka rawar gani shi ne na 1994 wanda ta kai zagayen kungiyoyi 16 da suka rage a gasar.

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

A wasannin matasa Najeria ta taka rawar gani inda tawagar Golden Eaglets ta matasa ‘yan kasa da shekara 17 ta ci kofin duniya karo biyar a 1985 da 1993 da 2007 da 2013 da kuma 2015.

Yayin da tawagar ta ci kofin Afirka karo biyu a 2001 da kuma 2007, ta kuma zo ta hudu a 2019.

Ita kuwa tawagar matasa ‘yan shekara 23 da ake kira Dream Team ita ce ta farko daga Afirka da ta ci lambar zinare a fagen kwallon kafa a wasannin Olympics.

Tawagar ce ta yi nasarar samun lambar zinare a 1996 da aka yi a Atlanta, sannan ta yi ta biyu a wasannin da aka yi a 2008 a Beijing.

Tawagar kwallon kafa ta mata kuwa ta Nigeria, Super Falcons ta lashe kofin Afirka sau 11 daga gasa 13 da aka yi.

Haka kuma Falcons din ta je gasar cin kofin duniya sau takwas, kuma na farko da ta fara zuwa shi ne a 1991, wanda ta fi yin abin kirki shi ne a 1999 wanda ta kai wasan dab da na kusa da karshe (quarter finals).

Ko a kwallon rairayiNajeriya ta taka rawar gani, inda ta lashe gasar Afirka a 2007 da kuma 2009, sannan ta yi ta biyu a 2006 da kuma 2011, ta kuma yi ta uku a 2015 sannan ta yi ta hudu a 2013.

Kwallon guragu da aka yanke musu kafa ta duniya – Tawagar Najeriya ta ‘yan wasan ta je gasar cin kofin duniya da aka yi a Mexico a 2018, bayan karo uku da ta kasa zuwa saboda karancin kudi.

Goodluck Obieze shi ne ya yi wa Najeriya kyaftin.

Sai dai kungiyoyin kwallon kafa na Nigeria ba su yi abin a-zo-a-gani ba a gasar Zakarun Afirka.

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Shooting Stars Sports Club ta Ibadan 3SC ita ce ta fara lashe wa Najeriya African Cup Winners Cup a 1976, bayan da ta yi nasara a kan Tonnerre Yahounde da ci 4-2 gida da waje.

Shekara 16 tsakani kungiyar ta ci CAF Cup, bayan da ta doke Villa SC ta Uganda 2-0 gida da waje, shekara daya tsakani Enugu Rangers ita ma ta ci CAF Cup bayan da ta yi nasara a kan Canon Yaounde da ci 5-2 gida da waje.

Daga nan ne sai da Najeriya ta yi shekara 38 kafin ta lashe kofin Zakarun Afirka wato CAF Champions League, inda Enyimba International ta lashe a 2003 da kuma 2004.

Tun daga nan, kungiyoyin kwallon kafar Nageriya ba su sake taka rawar gani a wasannin ba, inda a bana ma aka fara cire Kano Pillars sai Enyimba ma ta yi ban kwana da gasar ta koma Confederations Cup, ya yin da Enugu Rangers ta kai bantenta.

Sai dai wasan kwallon kafa a Najeriya ya ci karo da cikas a fanni da dama har da rigimar shugabancin NFF da aka yi ta yi har Fifa ta ce za ta dakatar da kasar.

‘Yan wasa a karo da dama sun yi zanga zanga kan kin biyansu hakkin wasa.

A ‘yan shekaru, Najeriya ba ta taka rawar gani a wasannin tsalle-tsalle da guje-guje na duniya ba, duk da kokarin da take yi a gasar Afirka idan aka kwatanta da kwazon da take yi a All Africa Games da sauran wasannin Afirka.

Hakkin mallakar hoto
BBC Sport

Wasannin Olympic – Najeria ta fara zuwa wasannin Olympic a 1952 bangaren tsalle-tsalle da guje-guje, haka kuma ta halarci gasar duniya ta The IAAF, inda ta yi bajinta a kakar 1989/99.

A kakar wasannin 1998, Gloria Alozie a tseren mita 100 da tsallen shinge da Falilat Ogunkoya a tseren mita 400 suka daga martabar Najeriya.

Haka ma a 1999 Charity Opara da Falilat Ogunkoya suka kare a mataki na daya da na biyu a tseren mita 400, tun daga nan kuma shiru kake ji.

A wasan matasa na nahiyar Afirka, Najeriya ta lashe gasa ta 12 da aka yi a birnin Addis Ababa, Ethiopia, inda ta ci lambar yabo ta zinare 12 da Azurfa takwas da tagulla 7.

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Wasan tsalle-tsalle da guge-guje – Wannan fanni Najeria ta yi fice wajen taka rawar gani da ‘yan wasanta ke gogayya da na Afirka da duniya.

Shekarar 1996 da 2000 ita ce Najeriya ba za ta manta da ita ba a wasannin tsalle tsalle da ta yi a Olympics.

‘Yan Najeriya Sunday Bada da Jude Monye da Clement Chukwu da kuma Enefiok Udo Obong sun taka rawar gani a 2000 inda suka lashe lambar zinare, shekara 12 tsakanin suka ci zinare, bayan da aka samu daya daga ‘yan tseren Amurka da laifin shan abubuwan kara kuzari duk da sune suka lashe tseren.

Wani wasan da Nigeria ta taka rawar gani shi ne wadanda aka yi a Atlanta a 1996, inda Chioma Ajunwa ta yi tsallen da ta lashe zinare tun farko da ya kai nisan mita 7.12.

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Wasan kwallon tebur – Wasan Kwallon tebur ya kai Najeriya mataki da dama, bayan da ta zama ta daya a Afirka, kuma tun samun ‘yancin kai a 1960 ‘yan wasan kasar maza da mata ke yin abin kirki a nahiyar da ma duniya.

‘Yan wasa kamar Atanda Musa da Segun Toriola da Sule Olaleye da Kazeem Nosiru da Monday Merountoun da kuma na kwanan nan Aruna Quadri sun ci wa kasar lambobin yabo a Afirka da duniya.

  • Nigeria ta kai zagayen gaba a tennis din teburi

A kakar 1998 zuwa 2008 Segun Toriola ya rike mataki na daya a Afirka a jerin wadanda ke kan gaba a kwallon tebur, haka shi ma Aruna Quadri bai bai wa kasarsa kunya ba, bayan an zabe shi tauraron dan wasa a 2017.

A bangaren wasannin mata Bose Kaffo da Biola Odumosu da kuma Funke Oshonaike sun bi sahun bajintar da maza suke yi, inda su uku suka lashe lambobin yabo a wasannin nahiyar Afirka da ya hada da All African Games da na Commonwealth Games.

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Kwallon kwando – A Kwallon kwando tawagar Najeriya, D’Tigers ta zama daya daga fitacciyar kwallon kwando a Afirka tare da Angola da Senegal.

Tawagar ta ci gaba da taka rawar gani, bayan kwarrarrun ‘yan wasan da take da su da wadanda ta rena da masu wasa a waje da suke bata gudunmawa.

Ita ma hukumar kwallon kwando ta Nigeria ta fada rikicin shugabanci, inda ake da shugabancin Tijjani Umar da da Musa Kida, wanda har yanzu ba a warware takaddamar ba, kuma har yanzu gasar kwallon kwando ta kasar na tsaye ba a buga wa.

ita ma tawagar mata ta kwallon kwanda ta bayar da tata gudunmawar, inda ta lashe lambar zinari a 2003 a All Africa Games da aka yi a Abuja, sannan ta je Olympic Games da aka yi a 2004 a Beijing.

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Damben boksin – Damben boksin kuwa daya ne cikin wasannin da suka daga martabar Najeriya inda ta dunga yin bajinta a wasannin Olympic Games da Commonwealth da All Africa Games.

A damben boksin na kwararru kuwa Najeriya ta samar da zakakuren zakarun duniya da suka hada da Dick Tiger da Hogan Bassey da kuma Samuel Peter.

Bayan da Najeriya ta samu ‘yancin kai a 1960, a shekarar 1963 Dick Tiger, ya dambace dan Amurka Gene Fulmer, ya kuma lashe kambun duniya ajin Middle weight.

Sun yi damben ne a Liberty Stadium, Ibadan, Najeriya, wasan da gidan talabijin na Afirka na farko ya nuna mai suna WNTV/WNBS, kuma karawar farko kai tsaye a wasa da aka nuna a Afirka.

A shekarar 1979, Davidson Andeh ya zama na farko dan Najeriya da ya lashe kambun duniya ajin Lightweight na matasa, bayan da ya yi nasara a kan dan Rasha a wasan da suka yi a birnin Belgrade, Yugoslavia.

Anthony Joshua, dan Najeriya da aka haifa a Burtaniya ya lashe kambun duniya ajin babban nauyi a 2018, sai dai yanzu ba shi ne ke kire da kumbunan ba.

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Damben gargajiya – Damben gargajiya ma galala ga rago an dade ana yinsa a Najeria tun kafin samun ‘yancin kai, wanda a lokacin sarakuna ne ke shirya shi da zarar sun yi baki ko kuma don fitar da gwani bayan an yi girbin amfanin gona.

Dambe yanzu ya bunkasa ana yinshi a ko’ina a fadin kasar, har ma ya shiga wasannin kasa wato National Sports Festival da ake yi.

‘Yan wasa a yanzu kan lashe mota ko babur da sauran kyaututtuka har da dubban kudi.

Kwallon tennis – Wasan kwallon tennis shi ma Najeria ta yi abin a-zo-a-gani musamman a nahiyar Afirka, Iro Ibrahim Yahaya shi ne mataimakin shugaban hukumar kwallon tennis na kasa ya kuma ce wasan na yin kololuwa duk da cikas da akan samu nan da can.

Hakkin mallakar hoto
AFP

Kwallon Badminton – Tawagar Najeriya ta zama zakara a 2018 a gasar da aka yi a Zambia, inda ta lashe lambar yabo hudu da ta hada da zinare biyu da azurfa biyu.

Dorcas Ajoke Adesokan ce ta yi nasara a kan Ogar Siamupangila a wasan mata ta lashe lambar yabo.

Haka kuma Adesokan ta yi wasa tare da Anu Opeyori a karawar ‘yan wasa bibiyu suka yi nasara.

Wasan nakasassu – Najeria ta fara zuwa karawar da aka yi a Barcelona a 1992, ko da yake kasar ba ta halarci Paralympics da aka yi tsakanin 1960 zuwa 1988, amma tun daga lokacin tana halartar sauran wasanni kuma tana taka gagarumar rawa.

Kwallon Polo – Wasan kwallon Polo ya karade sassa da sako na Najeria, kuma masu wasan sun wakilci kasar a nahiyar Afirka da duniya.

Ko da yake a baya ana yi wa wasan kallon na masu kudi ko masu sarauta da hakan ya hana wasu shiga kwallon polo da ta kai bunkasarsa ta yi tafiyar hawainiya.

Wasannin kasa – Bayan da aka yi shekara shida ba a gudanar da gasar wasanni ta kasa da ake kira National Sports Festival ba, babban birnin tarayya Abuja ya karbi bakuncin gasa ta 19.

Jihar Delta ce ta zama zakara a wasannin, bayan da ta lashe lambobin da suka hada da zinare 163 da azurfa 88 da tagulla 101 a wasannin kwana 10 da aka yi.

Ana hada wasannin ne saboda hada kan ‘yan kasa da zakulo ‘yan wasan da ke wakiltar kasar a fannin wasanni da dama.

Sai dai martabar wasan ta yi kasa sosai tun bayan wanda aka gudanar a Legas shekara shida da ta wuce.

Kammalawa– Da yake Najeriya na bikin cika shekara 59 da samun ‘yancin kai, akwai fatan da ake cewar nan da shekara mai zuwa abubuwa za su inganta a fagen wasanni.

Sai dai kuma masharhanta na cewa sai an tashi tsaye wajen bunkasa wasannin matasa tun daga tushe da karrama su da biyan ladan wasa a kan kari.

Haka kuma sai an samar da yanayin da masu ruwa da tsaki karbi wasanni daga hannun gwamnati da zuba jari a wasannin kasar da samar da cibiyar horo ta zamani da kowa zai iya zuwa ya gwada bajintarsa.

More News

EFCC na neman Yahaya Bello ruwa a jallo

Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati (Economic and Financial Crimes Commission) ta bayyana tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello a matsayin...

Mutane da dama sun mutu bayan motar fasinja ta taka bam a Borno

Akalla mutane 16 ne ake fargabar sun mutu yayin da wasu 20 suka jikkata bayan wata motar fasinja da ke kan titin Baga-Kukawa a...

Sojoji Sun Ceto Lydia Simon ĆŠaya Daga Cikin Ćłan Matan Chibok

Dakarun sojan Najeriya dake aiki da rundunar samar da tsaro ta Operation Desert Sanity III sun samu nasarar ceto, Lydia Simon É—aya daga cikin...

Gwamna da ƴansanda sun daƙile yunkurin EFCC na kama Yahaya Bello

A ranar Laraba ne Gwamnan Jihar Kogi, Usman Ododo, ya dakile wani yunkurin da Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati ta...