Kotu Ta Yanke Hukunci Kan Dokar Wa’azi a Kaduna

VOA Hausa

Sheik Halluru Maraya daya ne daga cikin manyan malaman addini musulunchi a Kaduna, kuma ya ce kamata ya yi gwamnati ta yi dokoki kan satar mutane ba wa’azi ba.

Ita ma kungiyar Kiristochi ta Nigeriya CAN ta ce hukuncin ya yi mata daidai. Rev. Joseph John Hayap shine shugaban kungiyar a Kaduna, ya ce tun farko suma sun yi niyar shigar da ‘kara amma lauyansu ya ce ‘kara ‘daya da aka shigar ya isa.

To sai dai mai taimakawa gwamnan jihar Kaduna ka harkokin addinin musulunci, Sheik Jamil Abubakar Albani, ya ce akwai kuskuren fahimta game da wannan doka, kasancewa har yanzu ba ta kai ga mai girma gwanan jihar Kaduna ba, kafin ya yi nazarinta domin matakin da zai ‘dauka.

Dama dai tun bayan kai wannan kudurin dokar wa’azi gaban Majalissar Dokokin Kaduna a shekarar 2016, darikar Fentacostal ta shigar da kara gaban babar kotun Kaduna wanda a ranar Laraba nan alkaliyar kotun mai Shari’a Hannatu Gwadah ta yanke hukuncin cewa kudurin ya sabawa kundin dokar kasa na 1999.

More News

Sojoji Sun Ceto Lydia Simon Ɗaya Daga Cikin Ƴan Matan Chibok

Dakarun sojan Najeriya dake aiki da rundunar samar da tsaro ta Operation Desert Sanity III sun samu nasarar ceto, Lydia Simon ɗaya daga cikin...

Gwamna da ƴansanda sun daƙile yunkurin EFCC na kama Yahaya Bello

A ranar Laraba ne Gwamnan Jihar Kogi, Usman Ododo, ya dakile wani yunkurin da Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati ta...

Gwamnatin Tarayya Za Ta Fara Rabon Gidaje 8925

Gwamnatin tarayya ta ce ta fara raba gidaje 8925  ga mutanen da suka nema kuma suka cancanci a basu a faɗin ƙasa baki ɗaya...

Ƴan Bindiga A Zamfara Sun Kashe Sakataren Jam’iyar PDP

Wasu ƴan bindiga da ba a san ko suwaye ba sun kashe, Musa Ille  sakataren jam'iyar PDP na ƙaramar hukumar Tsafe a jihar Zamfara. Zagazola...