Kotu ta soke zaben Sanata Dino Melaye | BBC news

Senator Dino Melaye

Hakkin mallakar hoto
@DINOMELAYE (INSTAGRAM)

Image caption

Da ma dai Sanata Melaye zai yi takarar gwamnan jihar Kogi

Kotun sauraron kararrakin zabe a garin Lokaja na jihar Kogi ta soke zaben Sanata Dino Melaye, wanda yake wakiltar shiyyar Kogi ta Kudu a Majalisar Dattawan Najeriya.

Yayin zaman kotun na ranar Juma’a ne aka soke zaben kuma aka umarci sake sabon zabe a shiyyar.

Daya daga cikin mutanen da suka kalubalanci Mista Melaye ne wato Sanata Smart Adeyemi na jam’iyyar APC ya shigar da kara a gaban kotun.

Bayan yanke wannan hukuncin Sanata Melaye ya bukaci magoya bayansa da su kwantar da hankalinsu, inda ya ce zai daukaka kara zuwa gaba.

Sanata Melaye ya fara zama dan majalisar wakilan kasar ne a shekarar 2007, inda yake wakiltar mazabar Kabba da Ijumu da ke jihar Kogi.

Sai da ya yi wa’adi biyu a majalisar wakilai kafin ya lashe zaben dan majalisar dattawa a shekarar 2015.

Kazalika a watan Yuni ne ya bayyana muradinsa na shiga takarar neman gwamnan jihar Kogi, wanda za a yi a watan Nuwamba mai zuwa.

More News

Majalisar dokokin jihar Kaduna ta nemi ma’aikatar kudin jihar ta miÆ™ata bayanan bashin da El-Rufai ya ciwo

Majalisar dokokin jihar Kaduna ta nemi ma'aikatar kudi ta jihar da ta miƙa mata cikakken bayani kan basukan  da gwamnatin tsohon gwamnan jihar, Nasiru...

An dakatar da ayyukan kamfanin jiragen sama na Dana Air

Festus Keyamo, ministan harkokin sufurin jiragen sama ya umarci hukumar FAAN dake lura da sufurin jiragen sama a Najeriya ta dakatar da ayyukan kamfanin...

Yahaya Bello Ya Bayyana Dalilan Da Ya Hana Shi Bayyana A Gaban Kotu

Tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello ya ce tsoron kamun  hukumar EFCC dake yaÆ™i da yiwa tattalin arzikin Æ™asa ne ya hana shi bayyana...

Ƴan sanda sun kama mutane biyu dake samarwa ƴan fashin daji makamai a jihar Kaduna

Rundunar Æ´an sandan jihar Kaduna ta ce tana tsare da wasu mutane biyu da ake zargi da safarar bindiga a jihar. A wata sanarwa ranar...