Kotu ta hana zaɓen shugabannin mazaɓu na jam’iyar PDP a Benue

Wata babbar kotu dake zamanta a ƙaramar hukumar Gboko ta jihar Benue ta hana jam’iyar PDP gudanar da zaɓen shugabannin mazaɓu a ƙananan hukumomi shida dake jihar.

Kotu ta dakatar da PDP daga cigaba da shirye-shiryen yin zaɓen shugabannin mazaɓu a ƙananan hukumomin da aka shirya gudanarwa ranar 10 ga watan Agustan 2024 a  Buruku, Gboko, Guma, Kwande, Ushongo, and Konshisha har sai an kammala binciken abun da ya jawo aka hargitsa zaɓen mazaɓun da aka yi na ranar 27 ga watan Yuli a ƙananan hukumomin.

Tun da farko, Sanata Emmanuel Oker Jev da sauran masu ƙara sun shigar da ƙorafi da ya kai ga kotun ta ɗauki matakin domin kare muradun sauran ƴaƴan jam’iyar da abun ya shafa.

Saboda haka ne kotun ta zartar cewa zaɓen shugabannin mazaɓu a yankunan da lamarin ya shafa ba zai gudana ba har sai an warware batun.

Amma kuma hukuncin kotun bai hana zaɓen shugabannin jam’iyar na jiha da aka shirya gudanarwa ranar 31 ga watan Agusta.

More News

Jam’iyar PDP ta dakatar da Dino Melaye

Jam'iyar PDP a jihar Kogi ta dakatar da Dino Melaye tsohon ɗantakarar gwamna a jihar kan zargin cin amanar jam'iya. Shugabannin jam'iyar PDP na mazaɓar...

Sojoji sun kashe gawurtaccen ɗan bindiga Kachalla Buzu

Dakarun rundunar sojan Najeriya sun samu nasarar kashe gawurtaccen ɗan bindiga Kachalla Halilu Sububu wanda aka fi sani da Kachalla Buzu. An kashe Kachalla ne...

Dakarun Najeriya sun hallaka ƴanbindiga a Neja

Rundunar sojin saman Najeriya ta hakala 'yanbindiga sama da 28 a yankin ƙaramar hukumar Shiroro dake jihar Neja.Wata sanarwa da mataimakin daraktan yaɗa labarai...

Tinubu ya gana da Sarki Charles

Shugaban ƙasa, Bola Ahmad Tinubu ya samu kyakkyawar tarba daga Sarki Charles na Birtaniya a fadar Buckingham a wata ziyara da yakai. Wannan ce ganawa...