Kotu ta hana Aminu Ado ayyana kansa a matsayin Sarkin Kano

Babbar Kotun jihar Kano ta hana Aminu Ado Bayero ayyana kansa a  matsayin Sarkin Kano har sai ta kammala sauraron ƙarar dake gabanta.

Kotun ta kuma umarci ƴan sanda su ƙwace iko da Gidan Sarki na Nasarawa, inda Aminu Bayero yake da zama tun bayan da ya dawo Kano a ranar Asabar.

Mai Shari’a, Amina Aliyu ita ta bayar da umarnin a ranar Litinin biyo bayan ƙarar da lauyan masu ƙara, Ibrahim Isa Wangida ya shigar gaban kotun a madadin waɗanda suke ƙara.

Kwamishinan shari’a na Kano, majalisar dokokin  jihar Kano da kuma kakakin majalisar dokokin su ne waɗanda suka shigar da ƙarar.

Waɗanda ake ƙara sun haɗa da Aminu Ado Bayero, Nasiru Ado Bayero, Ibrahim Abubakar II, Kabiru Muhammad Inuwa, Aliyu Ibrahim Gaya, Babban Sifetan Ƴan Sandan Najeriya, daraktan hukumar DSS da shugaban hukumar tsaro ta Civil Defence.

More from this stream

Recomended