Ko za ku iya hawa motar tasi mai tashi sama? | BBC news

Na’urarku na da matsalar sauraren sauti

Mota mai tashi ta Volocopter

Babu wani ma’aikaci da ba zai so a ce an samar da tsarin da zai iya zuwa da dawowa daga aikinsa cikin sauki ba.

Wato tsarin da zai kasance babu cunkoson ababen hawa, babu jinkiri – tabbas mutum zai so hakan.

Wannan wani albishir ne kan cewa fiye da kamfanoni 100 ne ke aiki kan kera motoci masu aiki da karfin lantarki wadanda ke iya tashi sama (eVTOL).

Kamar, jirage masu saukar ungulu, motocin ba su bukatar filin tashi da sauka, sai dai ba kamar jiragen na helikwafta ba, wadannan ba su da kara.

Sai dai da alama wannan mafarki zai iya daukan lokaci mai tsawo kafin ya zamo gaskiya. Masana sun ce wannan mota ba zai zama gama-gari ba sai a shekarun 2030.

Shin za su iya tafiya mai nisa?

Akwai dalilai da dama da suka sanya kamfanoni ke mayar da hankali kan wadannan motoci da za su iya zirga-zirga a ciki da kuma tsakanin birane.

Na farko, akwai yiwuwar za a samu masu son irin wadannan motoci da dama, sannan irin wadannan motoci za su iya tafiya mai tsawo a sama.

Yawancinsu na dauke da batiri wanda zai ba su damar tafiya a sama ta tsawon minti 30. A Jamus hakan na nufin cewa motar za ta iya tafiyar kusan mil 22 (Kilomita 35), a gudun kilomita 110, cikin awa guda.

An yi gwajin irin wannan mota a Singapore, ranar Talata.

Hakkin mallakar hoto
Lilium

Image caption

Zanen yadda motoci masu tashi za su rinka shawagi a samaniyar birnin New York

Wasu kamfanonin sun kara inganta motar ta hanyar yi mata fuka-fuki. Kamfanoni irin su Lilium na kasar Jamus suna da motar da kan iya tashi sama kai-tsaye, sannan za ta iya jujjuya fuka-fukanta kamar jirgin sama na asali.

Su ma kamfanonin kera jirage masu saukar ungulu a Birtaniya suna aiki kan kera mota mai tashi wadda ke da fukafuki, kuma suna sa ran za ta iya tafiyar sama da mil 100 a sama.

Sai dai irin wadannan kafanoni za su so ganin an samu ci gaba sosai a fasahar amfani da batura, wanda zai sanya irin wadannan motoci su yi amfani sosai.

A ina za a rinka tashi ana sauka?

Idan kana son fara sana’ar sufuri ta amfani da mota mai tashi, to kana bukatar tanadar isasshen wuri sauka da tashi, inda za a rinka masu caji ko kuma sauya batura – wadanda a turance ake kira veriports.

Wannan wani babban kalubale ne.

A manyan birane akwai karancin filaye. Akwai filayen saukan jirgin ‘Helikwafta’ sai dai kila ba zai isa ‘Helikwaftan’ da motoci masu tashi su rinka sauka a wurin ba.

WAdannan motoci za su iya samun wuraren da za su sauka a rufin gidaje, sai dai su iya kasancewa da tsada.

Koda ma an samu irin wadannan wurer, dole ne sai sun bi ka’idoji da dokoki, wadanda a yanzu ba a riga an samar ba.

Hakkin mallakar hoto
Lilium

Image caption

Yadda za a samar da wuraren saukan motoci masu tashi a manyan birane

Michael Cervenka, wani babban ma’aikaci a kamfanin Vertical Aerospace, ya ce daya daga cikin manyan dalilan da za su burge masu son sayen wadannan motoci shi ne ba su da kara. Karar motar a lokacin da take tashi sama ya yi kasa sosai idan aka kwatanta da na ‘helikwafta’.

Sannan kuma kararta kan yi kasa sosai a lokacin da take tafiya a sama.

Saboda haka wannan zai kwantar da hankalin wadanda ke da gidaje kusa da filayen saukan motoci masu tashi, sai dai za a iya samun wadanda ba za su kasancewa a kusa da ake samun yawan sauka da tashin jirage ba.

Sannan kuma da zarar aka samu hadri koda sau daya ne, mutane za su iya nuna adawa da saukar irin wadannan motoci a wuri mai cunkoson jama’a.

Mene ne rashin hadarinsu?

Masu lura da sufurin jirage a Turai da Amurka na aikin kan samar da dokoki da kuma ka’idojin da ya kamata wadannan motoci su cika.

Da zarar aka samar da ka’aidojin, akwai yiwuwar za a dauki shekaru ana gwajin wadannan motoci masu tashi, wanda zai iya lakume mililyoyin daloli.

Darell Swason, wani kwararre kan motoci masu tashi ya ce “Yawancin masu hada irin wadannan motoci da na tattauna da su na kokarin ganin sun samu amincewar kera su nan da shekara ta 2023.

Wata dama da suke da ita ita ce, motoci masu tashi sun fi saukin sha’ani idan aka kwatanta da ‘Helikwafta’ ko kuma jiragen fasinja. Saboda haka ba za su yi saurin samun matsala ba.

Hakkin mallakar hoto
Vertical Aerospace

Image caption

Karin injina za su rage wa motoci masu tashi yiwuwar samun matsala

Kamfanin sufuri na Uber, wanda ke da wani shiri na motoci masu tashi da ake kira Uber Air, ya ce ya kamata hadarin da ke tattare da tuka mota mai tashi ya gaza na tuka motar da aka saba har sau biyu.

To amma al’umma za su so ganin ana tsanteni game da sufurin wadannan motoci kamar yadda ake yi a harkar jiragen sama.

Motocin za su zamo ba su da nauyi sosai, sai dai kuma hakan zai sanya ya zamo da hadari idan ana tuka motocin a yanayi na isaka mai karfi.

Tsarin sufurin da zai tsaya a lokacin da ake fama da iska ba zai samu karbuwa ba a wurare eda dama na duniya.

Wane ne zai rinka lura da sufurin motoci masu tashi?

Na’urar tsara zirga-zirgar jiragen sama ita ce ke kula da sufurin jirage masu saukar ungulu a birane, kwararru kuma na ganin cewa wannan tsari zai iya hadawa da irin wadannan motoci.

Akwai rafuka da suka tsara ta tsakiyan birane da dama na duniya, wannan zai samar da hanya mai sauki ta sufurin irin wadannan motoci kasancewar babu al’umma a kasa.

To amma idan har za a rinka amfani da irin wadannan motoci sosai, to ya kamata a a samar da tsari na musamman da zai rinka kula da sufurinsu.

Hakkin mallakar hoto
Steve Wright

Image caption

Masani kan motoci masu tashi Steve Wright ya ce saukin da suke da shi zai sa su fi samun karbuwa

Hakan ne ma zai faru idan wannan bangare na sufuri ya cimma burinsa na samar da irin wadannan motovci marasa matuka.

Wadannan motoci dole ne su zamo za su iya ganewa a lokacin da suka kusanci wata motar a lokacin da suke tafiya.

Mr Swason ya ce “Ba wai a lokaci guda ne za a samu irin wadannan motoci kamar guda 5,000 suna shawagi a samniyar London ba nan da shekarar 2023”

“Za su rinka karuwa ne a hankali, ta yadda a haka za mu tabbatar abubuwa suna tafiya yadda ya kamata.”

Nawa za a kashe?

Ba a riga an kammala tsara yadda sufurin motoci masu tashi zai kasance ba. Amma dai ana sa ran za su rinka zirga-zirga a ciki da wajen birane ne bisa wata turba da aka tsara.

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Kamfani Uber ya yi alkawarin samar da mota mai tashi wadda ba ta kai tsadar rike mota ba

Tsarin sufurin motoci masu tashi na kamfanin Uber na ganin cewa wannan hanyar sufuri za ta zamo mai sauki ga al’umma. Za ta iya yin sauki fiye da mallakar mota.”

To amma, da farko dai masu kudi ne za su fi amfani da su.

Mr Wright ya ce “Masu hali, wadanda suka shirya biyan kudi tsugugu ne za su fara karbar wannan tsari.”

More News

ÆŠalibai a Jami’ar Jos na zanga-zanga saboda rashin wuta da ruwa

Wasu daliban jami’ar Jos da ke jihar Filato a ranar Alhamis sun gudanar da zanga-zangar nuna rashin amincewarsu da matsalar karancin ruwa da rashin...

MTN yana ƙoƙarin ƙara kuɗin kati da data a Najeriya

Katafaren kamfanin sadarwa na MTN na kokarin kara kudin katin waya da na data a Najeriya. Kamfanin sadarwa mafi girma a nahiyar Afirka ya ba...

Gwamnatin Kano Ta Rage ₦500,000 A Kuɗin Aikin Hajjin Bana

Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya sanar da yiwa maniyatan Aikin Hajji da suka fito daga jihar kyautar ₦500,000 domin su cika kuɗin...

Ƴan bindiga sun sace wani limami a jihar Kogi

Ƴan bindiga sun yi garkuwa da Quasim Musa babban limamin garin Iyara dake ƙaramar hukumar Ijumu ta jihar Kogi. Lamarin ya faru ne a ranar...