Ko Neymar zai dawo da martabarsa a PSG? | BBC news

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Ranar Asabar Neymar, ya koma buga wa Paris St Germain tamaula a gasar cin kofin Faransa da kungiyarsa ta buga da Strasbourg.

Neymar ya taka rawar gani har ma ya ci wani kayatacciyar kwallo mai ban sha’awa, sai dai magoya bayan PSG ko a jikinsu.

Kuma magoya bayan na PSG har ihu suka dunga yi wa dan wasan tawagar Brazil duk da kwallon da ya zura a raga, masu sharhi na cewar suna ganin Neymar ba dan wasansu bane.

Magoya bayan na cike da fushi da Neymar a lokacin da ya yi ta yunkurin sai ya bar Parc des Princes a kakar bana, lokacin da ake saye da sayar da ‘yan kwallon tamaula.

Ranar biyu ga watan Satumba aka rufe kasuwar Spaniya da Italiya da Faransa da kuma ta Jamus, ita kuwa ta Ingila tun 8 ga watan Agusat aka kammala hada-hada.

Neymar ya yi nacin sai ya bar PSG har da yin tayin zabtare Yuro miliyan 20 daga kudinsa, duk don ya bar Faransa da taka leda, kuma hakan ya harzuka magoya bayan PSG.

Wani batun da ya sa magoya bayan PSG suka dawo daga rakiyar Neymar shi ne lokacin da ya ce kwallon da ya ci PSG a gasar Zakarun Turai yana Barca tana daga cikin wadda ta fi kayatar da shi.

Magoya bayan PSG na ganin Neymar ya ci mutuncinsu a fannin kwallon kafa, shi ya sa suke saka masa da yi masa ihu a filin tamaula lokacin da yake wasa.

Daga baya mai rike da kofin gasar Faransa ta amincewa dan kwallon da ya koma inda yake bukata, sai dai hakan ya yi wahala domin dunbin kudin da aka sayo dan wasan a Barca.

Ya yi iya kokarinsa don ya koma Real Madrid ko kuma tsohuwar kungiyarsa Barcelona a bana, amma hakan bai yi wu ba, dole ya ci gaba da zama a PSG.

Sai dai kuma mahuntan PSG da suka sayo Neymar, Yuro miliyan 222 daga Barcelona a 2017, sun gargadi magoya baya da su dai na yi wa dan wasan ihu a lokacin da yake taka leda.

Sai dai hakan kamar bai shiga kunnensu ba, yayin da wasu ke ganin sai sun musguna masa kamar yadda ya zubar musu da kima a idon duniya.

Ranar Laraba 18 ga watan Satumba Paris St Germain za ta karbi bakuncin Real Madrid a wasan farko na cikin rukuni a gasar Champions League.

Wasannin makon farko da za a fara yi na cikin rukuni a gasar Champions League ta bana:

Ranar Talata 17 ga watan Satumba

  • Internazionale Milano da Slavia Prague
  • Olympique Lyonnais da Zenit St. Petersburg
  • Chelsea da Valencia
  • Ajax Amsterdam da Lille
  • Borussia Dortmund da Barcelona
  • Benfica da RB Leipzig
  • Napoli da Liverpool
  • Red Bull Salzburg da KRC Genk

Ranar Laraba 18 ga watan Satumba

  • Club Brugge da Galatasaray
  • Olympiacos da Tottenham
  • Atletico Madrid da Juventus
  • Bayer 04 Leverkusen da Lokomotiv Moscow
  • Bayern Munich da Crvena Zvezda
  • Paris Saint-Germain da Real Madrid
  • Dinamo Zagreb da Atalanta
  • Shakhtar Donetsk da Manchester City

More News

ÆŠalibai a Jami’ar Jos na zanga-zanga saboda rashin wuta da ruwa

Wasu daliban jami’ar Jos da ke jihar Filato a ranar Alhamis sun gudanar da zanga-zangar nuna rashin amincewarsu da matsalar karancin ruwa da rashin...

MTN yana ƙoƙarin ƙara kuɗin kati da data a Najeriya

Katafaren kamfanin sadarwa na MTN na kokarin kara kudin katin waya da na data a Najeriya. Kamfanin sadarwa mafi girma a nahiyar Afirka ya ba...

Gwamnatin Kano Ta Rage ₦500,000 A Kuɗin Aikin Hajjin Bana

Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya sanar da yiwa maniyatan Aikin Hajji da suka fito daga jihar kyautar ₦500,000 domin su cika kuɗin...

Ƴan bindiga sun sace wani limami a jihar Kogi

Ƴan bindiga sun yi garkuwa da Quasim Musa babban limamin garin Iyara dake ƙaramar hukumar Ijumu ta jihar Kogi. Lamarin ya faru ne a ranar...