Katsina: Yadda ‘yan bindiga suka sace gomman mata da yara

Image caption

‘Yan jihar Katsina da dama sun yi hijra zuwa jamhuriyar Niger

Da misalin karfe dayan daren ranar Litinin ne dai ‘yan bindigar su kimanin 120 suka shiga kauyen Wurma na karamar hukumar Kurfi a jihar Katsina, inda suka yi awon gaba da mata da dama sannan akasarin mutanen garin fantsama daji.

Shugaban karamar hukumar ta Kurfi, Alhaji Jabir Tsaure ya shaida wa BBC cewa akalla mutum fiye da 42 ne aka nema aka rasa.

An ce ‘yan bindigar sun yi awon gaba da matan aure da ‘yan mata da mata masu ciki da ma kananan yara ‘yan makarantar firamare.

Jabir Tsauri ya kuma tabbatar wa BBC batun cewa maharan sun kwashe fiye da awa uku suna cin karensu babu babbaka a kauyen, kafin su tasa keyar mutanen da ma dabbobi.

Wani mutum wanda ya shaida wa BBC cewa al’amarin ya shafi iyalansa, ya ce tuni masu garkuwar suka kira iyalai a kauyen na Wurmi suna neman kudin fansa.

Hare-haren masu garkuwa da mutane a jihar Katsina na daukar wani salo daban da na sauran jihohi, inda ake samun taron ‘yan bindiga su afka wa garuruwa.

Ko a watan Yuli ma sai da wasu ‘yan bindiga kimanin 300 suka far wa kauyuka uku na Kirtawa da Kinfau da Zamfarawan Madogara da ke yankunan kananan hukumomin Batsari da Safana, a jihar ta Katsina.

Bayanai da BBC ta samu daga mazauna yankunan jihohin na cewa kusan kullu yaumin sai an samu kauyukan da ‘yan bindigar suka far wa.

Za a iya cewa yanzu jihar Zamfara wadda a baya ta yi kaurin suna wajen hare-haren masu satar jama’a, ta mika wa makwabciyarta wato Katsina kambun.

Ko a baya-bayan nan sai da gwamnan jihar ta Katsina, Aminu Bello Masari ya ce, za a yi karancin abinci a yankunan da ake samun matsalar tsaron.

Manoma dai da dama ba sa iya zuwa gona saboda fargabar abin da ka iya faruwa da su idan suka shiga daji.

More News

Najeriya za ta dena shigo da man fetur a cikin watan Yuni – Dangote

Aliko Dangote mutumin da ya fi kowa arziki a Nahiyar Afirka ya ce Najeriya za ta daina shigo da man fetur a cikin watan...

An ceto mutane 9 daga wani ginin bene da ya ruguzo a jihar Niger

Mutane 9 aka samu nasarar cetowa daga wani ginin bene mai hawa É—aya da ya ruguzo a yankin Sabon Gwari dake garin Minna babban...

An yi faÉ—a tsakanin masu sayar da waya da sojoji a kasuwar Abuja

Rundunar ‘yan sandan babban birnin tarayya, ta tura jami’an leken asiri zuwa kasuwar Banex – wata kasuwar kayan lantarki da na’urorin sadarwa da ke...

Yawan Mutanen Da Suka Mutu A Wutar Da Wani Matashi Ya Cinnawa Wani Masallaci A Kano Sun  Karu Zuwa 16

Rundunar ƴan sandan jihar Kano ta ce yawan mutanen da suka mutu sakamakon wutar da wani ya cinnawa wani masallaci a ƙauyen Gadan a...