Kasuwar ‘yan kwallo: Makomar Zidane, Ancelotti, Pogba, Holgate, Koulibaly, Camavinga

Zinade Zidane

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,
Daman Real Madrid ta ce ta tsinkayi karshen zamanin Zinedine Zidane a kungiyar amma ba ta son sauya shi a karshen bazara in ji masani Guillem Balague

Kociyan Real Madrid Zinedine Zidane ya gaya wa ‘yan wasan kungiyar zai ajiye aikinsa a karshen kakar da ake ciki. (Jaridar Goal)

Hakan ya sa tuni kungiyar ta fara tunin daukar wanda zai maye gurbinsa, daga cikinsu akwai kociyan Everton Carlo Ancelotti da tsohon kociyan Juventus Massimiliano Allegri. (Jaridar Sunday Mirror)

Manchester United na son dan wasanta na tsakiya Paul Pogba, mai shekara 28, ya ci gaba da zama a kungiyar, ya kulla sabuwar yarjejeniya da ita, amma kuma tana tsoron yawan albashin da wakilin dan wasan na Faransa, Mino Raiola, ke neman a rika ba Pogban. (JaridarSunday Mirror)

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,
Paul Pogba ya ci wa Manchester United kwallo 38 a wasa 197 da ya yi mata

Everton ta ce a shirye take ta sayar da dan bayanta Mason Holgate, dan Ingila, mai shekara 24, domin ta samu kudin da za ta ganganda ta sayo dan bayan Napoli Kalidou Koulibaly, dan kasar Senegal, mai shekara 29. (Jaridar Football Insider)

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,
Zidane ne kawai kociyan da a tarihi ya dauki kofin Zakarun Turai uku a jere

Arsenal na fatan kasa Manchester City wajen daukar Ryan Bertrand, dan Ingila mai shekara 31. Dan bayan zai bar Southampton idan kwantiraginsa ya kare a karshen kakar nan. (Jaridar Mail ta Lahadi)

West Ham ta kasance ta gaba-gaba da za ta yi nasara wajen daukar mai tsaron ragar West Brom Sam Johnstone. Kafin yanzu ana danganta golan dan Ingila mai shekara 28 da shirin tafiya Tottenham. (Jaridar Football Insider)

Kociyan Barcelona da ke shan matsin lamba Ronald Koeman ya gana da shugaban kungiyar Joan Laporta, kuma ya ce za su sake ganawa a karshen kakar nan. (Jaridar Goal)

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,
Ronald Koeman na shan matsin lamba a kan rashin kokarin Barcelona

Eintracht Frankfurt na son nada tsohon dan gaban Real Madrid Raul a matsayin kociyanta a kaka ta gaba.(Jaridar Marca)

Real Madrid na son sayen dan wasan tsakiya na Faransa Eduardo Camavinga daga Rennes, amma kuma Arsenal ma na son matashin dan wasan mai shekara18. (Jaridar Marca)

Kungiyoyin Jamus Bayern Munich da Borussia Dortmund na sa ido a kan matashin dan wasan gaba na Sheffield United, haifaffen Canada, Daniel Jebbison mai shekara 17, na tawagar ‘yan kasa da shekara 18 ta Ingila. (90 Min)

Bristol City da Cardiff City da kuma Middlesbrough, kowacce na son daukar dan wasan gaba na Jamhuriyar Ireland James Collins, mai shekara 30, wanda kwantiraginsa da Luton Town zai kare. (Jaridar Mail ta Lahadi)

More News

MTN yana ƙoƙarin ƙara kuɗin kati da data a Najeriya

Katafaren kamfanin sadarwa na MTN na kokarin kara kudin katin waya da na data a Najeriya. Kamfanin sadarwa mafi girma a nahiyar Afirka ya ba...

Gwamnatin Kano Ta Rage ₦500,000 A Kuɗin Aikin Hajjin Bana

Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya sanar da yiwa maniyatan Aikin Hajji da suka fito daga jihar kyautar ₦500,000 domin su cika kuɗin...

Ƴan bindiga sun sace wani limami a jihar Kogi

Ƴan bindiga sun yi garkuwa da Quasim Musa babban limamin garin Iyara dake ƙaramar hukumar Ijumu ta jihar Kogi. Lamarin ya faru ne a ranar...

Delta: An dawo da gawarwakin sojojin da aka kashe Abuja don yi musu jana’iza

Gawarwakin sojojin da aka kashe a jihar Delta kwanan nan sun isa maƙabartar sojoji ta kasa da ke Abuja. Gawarwakin sun iso ne da misalin...