Kasuwar cinikin ‘yan kwallo: Makomar Werner, Haaland, Bale, Odegaard, Cavani, Almiron da Sarr

Timo Werner

Asalin hoton, Getty Images

Kocin Chelsea Thomas Tuchel ya bukaci mutumin da ya mallaki kungiyar Roman Abramovich ya yi amfani da dan wasan gaba na Jamus Timo Werner, mai shekara 25, a cikin yarjejeniyar musayar da za ta kai ga dauko Haaland daga Borussia Dortmund. (Sunday Express)

Dan wasan gaban Wales Gareth Bale ba ya cikin tsarin Real Madrid na kakar wasa mai zuwa, duk da yake dan kwallon mai shekara 31 ya ce yana shirin komawa kungiyar ta sifaniya a karshen zaman aron da ya kwashe kakar wasa daya yana yi a Tottenham. (Marca)

Asalin hoton, Huw Evans picture agency

Bale zai iya kasancewa cikin ‘yan wasa shida da Real Madrid za ta bari su tafi domin ta samu kudin da zai ba ta damar daukar dan wasan Faransa mai shekara 22 Kylian Mbappe, wanda ke Paris St-Germain, da kuma dan wasan Borussia Dortmund da Norway Erling Braut Haaland, mai shekara 20. (Sunday Mirror)

Manchester United za ta iya neman daukar dan wasan Watford da Senegal Ismaila Sarr, mai shekara 23, maimakon dan wasan Borussia Dortmund dan kasar Ingila mai shekara 21 Jadon Sancho idan ta yi nasarar daukar Haaland. (Sunday Express)

Sarr ya “kusa tafiya” Manchester United a bazarar da ta wuce, a cewar tsohon jami’in Watford Filippo Giraldi. (Goal)

An jirkirta tattaunawar da ake yi tsakanin Manchester City da dan wasanta Raheem Sterling game da sabunta kwangilarsa sai zuwa bazara, kuma ana ganin sauyin da dan wasan mai shekara 26 na wakilinsa na cikin dalilan da suka kawo jinkirin. (Star on Sunday)

Real Madrid za ta sayar ko kuma ta bayar da aron dan wasan Norway mai shekara 22 Martin Odegaard, wanda yanzu haka yake zaman aro a Arsenal, idan Zinedine Zidane ya ci gaba da zama a matsayin kocin kungiyar da ke buga gasar La Liga. (Football Insider)

Arsenal tana fargabar cewa farashin Odegaard’ zai tashi zuwa £50m a bazara, yayin da ake ganin kungiyoyi irinsu su Chelsea, Liverpool da PSG za su bi sahun wadanda ke son daukar dan wasan Real Madrid. (Star on Sunday)

Paris St-Germain na duba yiwuwar daukar golan Leeds United dan kasar Faransa Illan Meslier, mai shekara 21. (The National)

‘Yan wasan Newcastle United da dama sun fusata bisa kalamin da dan kasar Paraguay mai shekara 27 Miguel Almiron ya yi cewa yana son “murza leda a kungiyar da ke nuna kwazo sosai wajen wasa”. (Football Insider)

(BBC Hausa)

More News

Majalisar dokokin jihar Kaduna ta nemi ma’aikatar kudin jihar ta miÆ™ata bayanan bashin da El-Rufai ya ciwo

Majalisar dokokin jihar Kaduna ta nemi ma'aikatar kudi ta jihar da ta miƙa mata cikakken bayani kan basukan  da gwamnatin tsohon gwamnan jihar, Nasiru...

An dakatar da ayyukan kamfanin jiragen sama na Dana Air

Festus Keyamo, ministan harkokin sufurin jiragen sama ya umarci hukumar FAAN dake lura da sufurin jiragen sama a Najeriya ta dakatar da ayyukan kamfanin...

Yahaya Bello Ya Bayyana Dalilan Da Ya Hana Shi Bayyana A Gaban Kotu

Tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello ya ce tsoron kamun  hukumar EFCC dake yaÆ™i da yiwa tattalin arzikin Æ™asa ne ya hana shi bayyana...

Ƴan sanda sun kama mutane biyu dake samarwa ƴan fashin daji makamai a jihar Kaduna

Rundunar Æ´an sandan jihar Kaduna ta ce tana tsare da wasu mutane biyu da ake zargi da safarar bindiga a jihar. A wata sanarwa ranar...