Kasashen Nijer Da Benin Za Su Gana Da Najeriya Akan Sake bude Iyakokinta

A yayinda kasashen Nijer, Benin da Najeriya ke shirin tattauna hanyoyin sake bude iyakokin Najeriya a yau Alhamis, 14 ga watan Novemba, a Abuja babban Birnin Tarayyar Najeriya, gwamnatin Jamhuriyar Nijer ta sanar cewa, matakin na hukumomin Najeriya ya haddasa gibin dubban miliyoyin CFA a asusunta sakamakon tauyewar al’amura akan iyakokin kasashen biyu.

Da yake ganawa da wata tawagar jami’an asusun bada lamuni na FMI ko IMF a ranar talatar da ta gabata, ministan kudaden kasar Nijer Mamadou Diop ya sanar cewa, matakin rufe iyakokin Najeriya ya haifar da gibi a aljihun gwamnati, a cewar sa asarar billion 40 na CFA ne wannan mataki ya janyowa kasar Nijer saboda rashin samun kudaden da aka yi hasashen zasu shiga aljihun gwamnati ta hanyar awon kaya da biyan wasu diyyoyin kan iyakar kasar da Najeriya.

Ministan kudin kasar ta Nijer ya kara da cewa tuni ma’aikatan harkokin kudade suka bullo da wasu sabbin matakai don cike wannan gibi, kafin karshen shekara yayinda a dayan gefe wasu abokan hulda suka amince zasu tallafa da gudunmowar warware wannan matsala injishi.

Dr. Soly Abdoulaye masanin tattalin arziki a Nijer ya ce, faruwar wannan al’amari wani abu ne da ya kamata ya zamewa gwamnatocin Afrika irinsu Nijer darasi.

Ministan harkokin wajen Jamhuriyar Nijer Kalla Hankourao a karshen taron kungiyar CEDEAO da aka gudanar a makon jiya a Yamai, ya bayyana cewa kasashen Nijer da Najeriya da Benin zasu gudanar da taro a Abuja babban Birnin Tarayyar Najeriya, domin duba hanyoyin sassauta wannan mataki da ya jefa miliyoyin talakawa cikin halin kuncin rayuwa.

Ga cikakken rahoton Wakilin muryar Amurka a yamai Souley Moumouni Barma.

More News

Majalisar dokokin jihar Kaduna ta nemi ma’aikatar kudin jihar ta miÆ™ata bayanan bashin da El-Rufai ya ciwo

Majalisar dokokin jihar Kaduna ta nemi ma'aikatar kudi ta jihar da ta miƙa mata cikakken bayani kan basukan  da gwamnatin tsohon gwamnan jihar, Nasiru...

An dakatar da ayyukan kamfanin jiragen sama na Dana Air

Festus Keyamo, ministan harkokin sufurin jiragen sama ya umarci hukumar FAAN dake lura da sufurin jiragen sama a Najeriya ta dakatar da ayyukan kamfanin...

Yahaya Bello Ya Bayyana Dalilan Da Ya Hana Shi Bayyana A Gaban Kotu

Tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello ya ce tsoron kamun  hukumar EFCC dake yaÆ™i da yiwa tattalin arzikin Æ™asa ne ya hana shi bayyana...

Ƴan sanda sun kama mutane biyu dake samarwa ƴan fashin daji makamai a jihar Kaduna

Rundunar Æ´an sandan jihar Kaduna ta ce tana tsare da wasu mutane biyu da ake zargi da safarar bindiga a jihar. A wata sanarwa ranar...