KAROTA sun gargadi masu a-daidaita-sahu da su daina amfani da iskar gas maimakon fetur



Hukumar kula da zirga-zirgar ababen hawa ta jihar Kano, KAROTA, ta bayar da gargadi kan amfani da iskar gas a maimakon man fetur a a-daidaita-sahu.

Shugaban hukumar KAROTAr Faisal Mahmud-Kabir ya bayyana haka ne a wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a hukumar Nabilusi Abubakar ya fitar ranar Laraba a Kano.

Malam Mahmud-Kabir ya yi gargadin cewa amfani da iskar gas a kekunan a-daidaita-sahu maimakon man fetur yana da hadari domin yana iya fashewa da kuma haddasa asarar rayuka.

Ya kuma bayyana cewa duk wanda aka kama yana yin irin wannan za a kama shi.

More from this stream

Recomended