Karin Mutum 187 Sun Kamu Da COVID-19 a Najeriya

0

VOA Hausa

Gaba dayan adadin wadanda aka tabbatar sun kamu da cutar COVID-19 a Najeriya ya kai 58,647 zuwa daren Talata, 29 ga watan Satumba, a cewar hukumar NCDC da ke sa ido kan cututtuka masu yaduwa.

A bayanan da ta ke fiddawa a kowace rana a shafinta na Twitter, hukumar ta NCDC ta ce an samu karin mutum 187 da suka kamu da cutar a ranar.

A cewar hukumar, cikin mutum 58,647 da suka kamu da cutar, mutum 49,937 sun warke kuma an sallame su daga asibiti yayin da mutum 1,111 ne suka mutu.

Hukumar ta kuma ce an samu karin adadin ne daga jihohi 13, ciki har da Jihar Legas da mutum 74. Sai kuma jihar Filato da ke biye da mutum 25.

Sauran jihohin sun hada da Rivers (25), Gombe (19), FCT (19), Osun (10), Kaduna (5), Borno (3), Ogun (2), Katsina (2), Nasarawa (1), Bayelsa (1), Edo (1)

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here