Kano: An ayyana ƙwacen waya a matsayin laifin “fashi da makami”

A martanin da hukumar tsaro ta jihar Kano ta mayar kan karuwar satar wayar tarho, ta ayyana hakan a matsayin ta’asar “fashi da makami.”

Ta ba da umarnin cewa duk wani mutum ko kungiyar da aka samu da irin wannan laifin a mayar da shi a matsayin ‘yan fashi da makami.

A makonnin baya-bayan nan dai birnin Kano ya gamu da yawaitar matsalar sace-sacen waya.

Sama da mutane 90 ne ‘yan sanda suka kama, kuma an samu rahoton kashe mutane 10 da barayin waya suka yi.

Mutane dai sun nuna damuwarsu kan yadda ake sake samun wadanda ake zargin, wadanda sukan sake fitowa kan tituna ‘yan watanni kadan bayan tsare su, lamarin da ke nuni da cewa tuhumar satar da ake yi a halin yanzu da kuma daurin watanni shida a gidan yari ko kuma tarar da ake yi musu ba su isa ya hana su ba.

A cewar kwamishinan yada labarai da harkokin cikin gida na jihar, Malam Muhammad Garba, majalisar tsaro karkashin jagorancin gwamna mai barin gado Abdullahi Umar Ganduje, ta fahimci tsananin girman lamarin da kuma wajabcin daukar tsauraran matakai.

Majalisar ta amince da kafa wata runduna ta musamman a cikin tsarin tsaro domin yakar wannan barazana tare da wasu nau’ikan laifuka a jihar.

More News

Majalisar dokokin jihar Kaduna ta nemi ma’aikatar kudin jihar ta miƙata bayanan bashin da El-Rufai ya ciwo

Majalisar dokokin jihar Kaduna ta nemi ma'aikatar kudi ta jihar da ta miƙa mata cikakken bayani kan basukan  da gwamnatin tsohon gwamnan jihar, Nasiru...

An dakatar da ayyukan kamfanin jiragen sama na Dana Air

Festus Keyamo, ministan harkokin sufurin jiragen sama ya umarci hukumar FAAN dake lura da sufurin jiragen sama a Najeriya ta dakatar da ayyukan kamfanin...

Gwamantin Kano na kashe naira biliyan 1.2 duk wata don samar da ruwan sha—Kwamishina

Gwamnatin jihar Kano na kashe kimanin naira biliyan 1.2 duk wata don samar da ruwan sha na tafi da gidanka a cikin babban birnin...

Yahaya Bello Ya Bayyana Dalilan Da Ya Hana Shi Bayyana A Gaban Kotu

Tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello ya ce tsoron kamun  hukumar EFCC dake yaƙi da yiwa tattalin arzikin ƙasa ne ya hana shi bayyana...