Kanar Goita zai jagoranci gwamnatin Mali | Labarai

0
Hakan na nufin cewar, Kanar Goita zai jagoranci Malin, a yayin da ake shirin sake mayar da ita turbar demokradiyya, bayan kwace mulkin kasar da yayi a wannan mako mai karewa.
Kotun tsarin mulki ta bayyana cewar, ta zartar da hakan ne domin rufe gibin rashin shugaban kasa, bayan murabus na shugaban rikon kwarya Bah Ndaw.
A ranar Litinin ne dai, dakarun kasar suka capke tare da tsare Ndaw da framinista Moctar Ouane, kafin sakinsu ranar Alhamis bayan sun sanar da yin murabus daga mukamansu.
Kafin hambarar da gwamnatin nasu dai, Ndaw da Ouane na jagorantar gwamnatin riko, bayan kifar da mulkin zababben shugaba Boubacar Keita a watan Augustan bara.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here