Kamfanin M&S baya samun ciniki

Marks & Spencer store

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Rashin bukatar kayayyakin da kamfanin Marks and Spencer ke samarwa da suka hada da tufafi da kayan kawa na gidaje ne dalilin da sa ba ya samun tagomashin azo a gani ba a wannan shekara.

Kamfanin ya sanar da cewa kayan abinci da dangoginsu da suke samarwa na kara karbuwa, to amma bukatar tufafi ta ragu matuka.

A yanzu dai M&S na kokarin yin wasu sauye-sauye da nufin inganta kasuwancin kamfanin.

Babban kalubalen shi ne babu riba a cinikin da aka yi a rubu’i na biyu a wannan shekara.

  • Yarinyar da kashinta ke yawan karyewa, kuma tana son rawa
  • ‘Tasirin Iran ya wuce na Saudiyya a Gabas Ta Tsakiya’

Harajin da ya ke biya ya tashi zuwa kashi 17 cikin 100, yayin da ya samu faduwar kusan kashi 3 cikin 100 a bangaren tufafi.

A watan Satumba da ya wuce kamfanin ya karya farashin tufafi da kayan kawata gida da nufin jan hankalin abokan hulda.

To sai dai abin mamakin shi ne an samu raguwar kusan kashi 5 cikin 100 na kayan da aka karya farashinsu, idan aka kwatanta da kashi 4 cikin 100 a shekarar da ta gabata.

M&S ya amince akwai babban kalubale a gabansa na farfado da darajar kayayyaki da jan hankalin abokan hulda da amfani da sabbin dabarun kasuwanci.

Musamman yanzu da M&S ya ke fuskantar wata matsalar yadda ake samun takwarorinsa masu kayan tufafi da kawata gida masu inganci da tafiya da zamani kamar kamfanin Primark, sai kuma Asos da ke shafin internet.

Wata sabuwar dabarar kasuwanci da M&S ya bullo da ita, shi ne kai wa abokan hulda kayan abincin da suka saya ta internet a duk inda suke dan haka ya amince da kamfanin dakon kaya na Ocado ya shigo su yi aikin tare.

Hakkin mallakar hoto
Newscast

More News

Majalisar dokokin jihar Kaduna ta nemi ma’aikatar kudin jihar ta miÆ™ata bayanan bashin da El-Rufai ya ciwo

Majalisar dokokin jihar Kaduna ta nemi ma'aikatar kudi ta jihar da ta miƙa mata cikakken bayani kan basukan  da gwamnatin tsohon gwamnan jihar, Nasiru...

An dakatar da ayyukan kamfanin jiragen sama na Dana Air

Festus Keyamo, ministan harkokin sufurin jiragen sama ya umarci hukumar FAAN dake lura da sufurin jiragen sama a Najeriya ta dakatar da ayyukan kamfanin...

Yahaya Bello Ya Bayyana Dalilan Da Ya Hana Shi Bayyana A Gaban Kotu

Tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello ya ce tsoron kamun  hukumar EFCC dake yaÆ™i da yiwa tattalin arzikin Æ™asa ne ya hana shi bayyana...

Ƴan sanda sun kama mutane biyu dake samarwa ƴan fashin daji makamai a jihar Kaduna

Rundunar Æ´an sandan jihar Kaduna ta ce tana tsare da wasu mutane biyu da ake zargi da safarar bindiga a jihar. A wata sanarwa ranar...