Connect with us

Hausa

Kalli hotunan barnar da rikicin ‘yan Shi’a da ‘yan sanda ya haifar | BBC Hausa

Published

on

Hakkin mallakar hoto
KOLA SULAIMON

Wani dan sanda na tafiya a gefen wata mota da masu goyon bayan shugaban Kungiyar ‘Yan Uwa Musulmi, Sheikh Ibrahim Zakzaky suka kona a kusa da harabar majalisar dokokin Najeriya a Abuja, babban birnin kasar ranar 9 ga watan Yulin 2019.

Hakkin mallakar hoto
KOLA SULAIMON

Masu goyon bayan shugaban ‘yan Shi’an da ke tsare sun yi arangama da jami’an tsaro kuma mutane da yawa sun samu raunuka ciki har da ‘yan sanda biyu kamar yadda hukumomi da shaidu suka bayyana.

Hakkin mallakar hoto
KOLA SULAIMON

‘Yan kwana-kwana na kokarin kashe wutar da ke fitowa daga wata mota bayan arangamar tsakanin jami’an tsaro da magoya bayan Sheikh Ibrahim Zakzaky.

Hakkin mallakar hoto
KOLA SULAIMON

Mummunar arangamar ta jikkata mutane. Wani takalmi a wurin da jini ya zuba yayin rikicin tsakanin jami’an tsaro da mabiya Ibrahim Zakzaky.

Hakkin mallakar hoto
KOLA SULAIMON

An lalata motoci da gine-gine a lokacin taho-mu-gaman. Nan wani wurin tsayuwar ‘yan sanda ne da masu zanga-zangar suka lalata ranar 9 ga watan Yulin 2019.

Hakkin mallakar hoto
KOLA SULAIMON

Kungiyar ‘Yan Uwa Musulmin dai sun musanta zarge-zargen rundunar ‘yan sanda na cewa magoya bayan Ibrahim Zakzaky sun harbi ‘yan sandan uku. Wannan wata motar ‘yan sanda ce da masu zanga-zangar suka lalata.

Hakkin mallakar hoto
KOLA SULAIMON

Wani wurin duba motoci da masu zanga-zangar suka lalata sannan suka yi rubutun nuna kin jinin tsare shugaban kungiyarsu Ibrahim Zakzaky.

Facebook Comments
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Hausa

Kamfanoni Guda 4 Sun Fara Samar Da Madara A Najeriya

Published

on

Duk a cikin manufar babban bankin Najeriya wato CBN na hana shigo da madara daga waje, wasu kamfanonin kasar guda hudu sun soma sarrafa madara yar gida.

Gwamnan CBN Godwin Emefiele wanda ya bayyana hakan a Abuja a ranar Alhamis, 19 ga watan Satumba, ya bayar da sunayen kamfanonin.

KamfaNonin sune FrieslandCampina WAMCO, Neon Agro, Chi Limited da Irish Dairy. Yace sun rigada sun nuna ra’ayin zuba jari a kamfanin Bobi Grazing Reserve a jihar Neja.

Bobi Grazing Reserve dake a yankin karamar hukumar Mariga ya kasance daga cikin masana’antun kiwo 26 karkashin wani shirin bunkasa harkar kiwo da gwamnatin jihar Neja ke yi tare da hadin gwiwar CBN.

A halin yanzu gwamnan CBN yace FrieslandCampina WAMCO da Neon Agro sun amince da kowannen su zai siya fili mai fadin hekta 10,000, sannan Chi Limited da Irish Dairy zasu siya hekta 4,000 kowannen su don kafa shirin sarrafa madara.

Gwamnatin jihar zata ajiye sauran hekta 3,000 don gudanar da shirin cigabanta.

A ranar Talata, 18 ga watan Satumba, Mista Emefiele yace kamfanin FrieslandCampina WAMCO ta gyara fili hekta 695 sannan anyi shuke shuke a hekta 190 don shirin kiwo.

Har ila yau, kamfanin ta kammala shuke shuken iri masu inganci, famfunan solar yayin da ake jiran hada kayan aikin tatse madara.

A wani lamari makamancin haka, yace Chi Limited har ila yau ta sa hannu a kwangilan shuke shuken fili hekta 4,000 da aka samar mata.

Yace Gwamnatin Jihar Neja ta gyara da kuma katange hekta 63 a wurare biyu.

Yace wurin zai kasance da cibiyar yan sanda, asibitin dabbobi, makarantar firamare, yayinda ake shiri gina cibiyar lafiya. hakazalika a yazu aa kan shuke-shuke.

Facebook Comments
Continue Reading

Hausa

NFF da kulob din Roma sun kulla yarjejeniya | BBC Hausa

Published

on

Shugabannin NFF (Amaju Pinnickda) da AS Roma (Jim Pallottane) ne da mataimakansu a wurin taron kulla yar

Hakkin mallakar hoto
NFF

Image caption

Shugabannin NFF (Amaju Pinnickda) da AS Roma (Jim Pallottane) ne da mataimakansu suka halarci taron

Hukumar Kwallon Kafa Ta Najeriya NFF ta kulla yarjejeniyar aiki tare da kungiyar kwallon kafa ta AS Roma mai buga gasar Serie A ta Italiya.

Bisa ka’idojin yarjejeniyar, Roma da Hukumar Kwallon Kafa Ta Najeriya za su rika gudanar da harkokin da suka shafi wasanni a ciki da wajen fili, kamar yadda bangarorin biyu suka bayyana ranar Juma’a.

Bangarorin biyu za su rika taimaka wa juna wajen ci gaban harkokin wasanni da suka hada da shawarwari game da horar da matasan ‘yan wasa daga Najeriya da kuma koyar da kulob-kulob a Najeriya yadda za su rika tafiyar da shafukansu na sada zumunta.

Ita kuma NFF za ta taimaka wa Roma wajen gina nata harkokin a Najeriya.

Kazalika, a watanni masu zuwa jami’an hukumar ta NFF za su yi tattaki zuwa birnin Rome domin ganin yadda kungiyar matasa ta Roma ke gudanar da wasanninsu.

Hakan zai ba su dama wurin gina matasa da kuma kungiyoyinsu a harkar wasanni a gida Najeriya.

Shugaban kungiyar ta Roma Jim Pallotta ya ce tun a 2018 suka fara aiki da Super Eagles yayin gasar cin Kofin Duniya a kasar Rasha.

“Rukunin ma’aikatanmu sun fara aiki tare da Super Eagles a 2018 a shafukan sada zumunta da kuma lokacin gasar Kofin kasashen Afirka, wanda aka fara da maudu’in #ForzaSuperEagles.

“Mu ne kungiya ta farko daga wajen Najeriya da ta bude shafin Twitter cikin harshen Pidgin mai shelkwata a Lagos.”

Kungiyar za ta duba yiwuwar buga wasan bude ido a Najeriya tare da bude makarantar horar da wasanni.

Facebook Comments
Continue Reading

Arewa

Najeriya ta rufe ofishin kungiyar Action Aid kan Boko Haram | BBC Hausa

Published

on

Aid bags

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Rundunar sojin Najeriya ta dakatar da ayyukan kungiyar agaji ta kasa da kasa, Action Aid mai yaki da talauci bisa zargin kungiyar da hannu wajen samar wa Boko Haram abinci da magunguna.

Rundunar ta ce ta gargadi kungiyar agajin kan agazawa Boko Haram a yankin arewa maso gabashin kasar.

Action Against wacce ta musanta zarge-zargen, ta ce taimakon take samar wa mutanen da rikici ya shafa na fuskantar kalubale.

Rikicin kungiyar ‘yan-tada-kayar-bayan da aka shafe shekara 10 ana yi ya halaka mutane sama da 30,000.

Fiye da mutum miliyan biyu kuma sun rasa matsugunansu.

Wata gamayyar kungiyoyin farar hula na taimakawa gwamnati wajen agazawa mutanen da aka tilastawa barin gidajensu.

A shekarar 2018, rundunar sojin kasar ta taba zargi hukumar kula da kananan yara ta MDD, UNICEF da zama ‘yar leken asirin masu tada-kayar-baya, abin da ya sa ta haramta kungiyar wacce a nata bangaren ta musanta zarge-zargen.

Sai dai daga baya, gwamnatin ta janye haramcin.

Cikin wata sanarwa, Action Aid ta ce tana samar da taimako ne ba tare da wata manufa ta daban ba ga miliyoyin mutane a jihar Borno ta hanyar samar masu da kayayyakin agaji ga mutanen da rikici ya fi shafa musamman mata da yara kanana.

Kungiyar ta ce sojoji, ba tare da wata sanarwa ba, sun bukaci ta rufe ofishinta da ke birnin Maiduguri a jihar Borno.

Cikin watan Yuli, Action Aid wacce ke da mazauni a Paris ta ce ma’aikatan ta masu ba da ceto sun shiga hannun masu garkuwa a Najeriya.

An ga ma’aikatan shida cikin wani bidiyo, inda daya daga cikinsu take kira ga gwamnatin kasar da al’ummar kasar waje da su sa baki a kubutar da su.

Kawo yanzu, babu wanda ya san inda ma’aikatan suke.

Babu kuma wata kungiya da ta fito ta ce ita ce ta sace ma’aikatan.

A shekarar 2015, Boko Haram ta kwace iko da kaso mai tsoka na Borno abin da ya ba ta damar fadada ayyukanta zuwa makwabtan kasashe.

Yakin kawo karshen masu tada-kayar-baya da sojoji suka kaddamar ya sa gwamnati kwato mafi yawan yankunan da suka fada hannun Boko Haram.

Sai dai a baya bayannan, masu tada tarzomar sun fadada kai harin kunar bakin wake da sace-sacen jama’a domin cimma muradunsu.

Daya daga cikin hare-hare mafi muni da ta kai shi ne kan makarantar ‘yan mata ta Chibok da ke arewa maso gabashin kasar lokacin da aka yi garkuwa da dalibai ‘yan mata 276.

Da yawa daga cikinsu sun kubuta, amma dai har yanzu ba a kai ga gano inda wasu 100 suke ba.

Rahotanni na cewa tun daga 2013, Boko Haram ta sace mutane fiye da 1,000.

Facebook Comments
Continue Reading
Advertisement
Advertisement

Trending

%d bloggers like this: