Kalaman Janar Buratai sun janyo ka-ce-na-ce tsakanin masana tsaro

Lokacin da yake gabatar da jawabi, Janar Buratai ya ce “rashin kwazo da rashin azama wajen yin fada, na wasu daga cikin hafsoshi da sojoji na daga cikin abubuwan dake haddasa musu koma baya a fafatawar da ake yi yanzu.”

Janar Buratai, wanda ya ce ko da baya ga zagon ‘kasa da ake yi musu, akwai kuma tabbatattun shaidu dake nuna koma bayan da ake fuskanta a baya-bayan nan nada alaka da rashin kishin ‘kasa da kuma rashin kishin aikin soja.

Tuni dai wannan jawabi na janar Buratai ya haddasa cece-kuce tsakanin masana tsaro da kuma tsaffin jami’an tsaron.

Dakta Kabiru Adamu, na daga cikin wadanda ke ganin rashin dacewar wannan jawabi na Buratai, inda ya ce ko da kuwa akwai matsalar tsaro bai kamata ba hafsan Soja ya fito ya yi irin wadannan kalaman ba.

Sai dai kuma tsohon hafsa a rundunar sojan Najeriya, majo Shu’aibu Bashir Galma, na ganin kalaman da janar Buratai ya yi na bisa hanya.

More News

Yahaya Bello Ya Bayyana Dalilan Da Ya Hana Shi Bayyana A Gaban Kotu

Tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello ya ce tsoron kamun  hukumar EFCC dake yaƙi da yiwa tattalin arzikin ƙasa ne ya hana shi bayyana...

Ƴan sanda sun kama mutane biyu dake samarwa ƴan fashin daji makamai a jihar Kaduna

Rundunar ƴan sandan jihar Kaduna ta ce tana tsare da wasu mutane biyu da ake zargi da safarar bindiga a jihar. A wata sanarwa ranar...

An kori sojojin Najeriya biyu saboda satar kebul a matatar Dangote

Rundunar sojin Najeriya ta tabbatar da korar wasu sojoji biyu da ake zargi da satar igiyoyin sulke a harabar matatar Dangote da ke jihar...

Magoya bayan APC da dama sun koma NNPP a Kano

Jam'iyar NNPP ta karɓi magoya bayan jam'iyar APC da dama a jihar Kano. Mataimakin gwamnan jihar Kano, Aminu Abdul Salam Gwarzo shi ne ya karɓi...