Jirgin saman kamfanin Xejet ya zame daga kan titin filin jirgin saman Lagos

A ranar Asabar ne wani jirgin sama mallakin kamfanin Xejet ya zame daga kan titin filin jirgin saman Murtala Muhammad dake Lagos.

Hukumar NSIB dake karewa tare binciken haɗura a Najeriya ita tabbatar da haka cikin wata sanarwa da ta fitar ranar Asabar..

Hukumar ta ce jirgin wanda ya taso daga Abuja ya zame daga kan titin filin jirgi na 18L lokacin da yake sauka a Lagos inda ya ci birki a cikin ciyawa.

A cewar hukumar jirgin mai namba 5NBZZ na ɗauke da fasinjoji 52 lokacin da lamarin ya faru.

Hakan na faruwa ne makonni bayan da wani jirgin saman kamfanin Dana Air shima ya zame da kan titin filin jirgin lokacin da yake sauka a filin jirgin saman na Lagos.

More from this stream

Recomended