Jirgin Max Air dauke da alhazan Jigawa ya yi saukar gaggawa a Kano

Rukunin farko na alhazan jihar Jigawa sun tsira daga hatsarin jirgin sama bayan da jirgin saman Max Air da suke ciki ya yi saukar gaggawa a Kano.

Jirgin ya yi saukar gaggawa ne sakamakon walkiya da tsawa da ta fada masa lokacin da yake tafiya a sama.

Jirgin kirar Boeing 747 ya tashi daga filin jirgin sama dake Dutse da misalin karfe 04:45 na yamma kafin daga bisani ya yi saukar gaggawa a filin jirgin saman Mallam Aminu Kano dake Kano.

Alhazan da ke cikin jirgin su 559 sune kason farko na alhazan jihar su 1625 da za suyi aikin hajjin bana.

Mai magana da yawun kamfanin jiragen saman Max Air a Kano, Bello Ramadan ya tabbatar da faruwar lamarin a daren jiya. Inda ya ce lamarin ya faru ne bayan da walkiya da tsawa ta fadawa jirgin inda hakan ya shafi gilashin hagu na mataimakin matukin jirgin.

Tuni aka sauyawa alhazan wani jirgin da ya dauke su zuwa kasa mai tsarki.

More News

EFCC na neman Yahaya Bello ruwa a jallo

Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati (Economic and Financial Crimes Commission) ta bayyana tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello a matsayin...

Mutane da dama sun mutu bayan motar fasinja ta taka bam a Borno

Akalla mutane 16 ne ake fargabar sun mutu yayin da wasu 20 suka jikkata bayan wata motar fasinja da ke kan titin Baga-Kukawa a...

Sojoji Sun Ceto Lydia Simon ĆŠaya Daga Cikin Ćłan Matan Chibok

Dakarun sojan Najeriya dake aiki da rundunar samar da tsaro ta Operation Desert Sanity III sun samu nasarar ceto, Lydia Simon É—aya daga cikin...

Gwamna da ƴansanda sun daƙile yunkurin EFCC na kama Yahaya Bello

A ranar Laraba ne Gwamnan Jihar Kogi, Usman Ododo, ya dakile wani yunkurin da Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati ta...