Jinsin jakai na barazanar karewa a duniya | BBC Hausa

Jakuna uku

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Fasa-kwauri da cinikin fatun jakai, abu ne da ke ci gaba da jan hankalan masu ruwa da tsaki da mahukunta a fadin duniya.

Sun ce yanka dabbobin ba ya rasa nasaba da gagarumin neman da ake masu a kasar China wajen hada magungunan gargajiya.

A makon jiya ne majalisar dokokin Nijeriya ta yi zaman jin ra’ayoyin jama’a kan wani kudurin doka na Honarabul Garba Datti Muhammad da ke neman haramta yanka da fataucin jakai zuwa ketare.

Cikin mahalarta zaman, har da jami’an wata gidauniya ceto jakai mai fafutuka don inganta rayuwar jakan da alfadarai da ma mutane ta Burtaniya.

Simon Pope, babban jami’i a gidauniyar Donkey Sanctuary ta kasar Birtaniya ya ce abin bakin ciki ne idan aka yi la’akari da amfanin jaki a rayuwar dan adam a matsayin wani abun sufuri kamar mota.

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Mista Pope ya kuma ce mafi yawan fatun da ake safara suna fitowa ne daga Afirka.

Ya ce “Najeriya musamman na jan hankalin masu sayen fatar jakai saboda yawansu a nan.”

Ya kuma ce a kalla akwai jakai miliyan daya da dubu dari uku a kasar.

“Sai dai wani dan kasuwa ya bayyana cewa ana yanka a kalla jakai dubu biyu da dari biyar a kasuwarsu kullum”, in ji Mista Pope.

Hakan kuma ya nuna ana kashe jakai kusan dubu dari shida duk shekara.

Ya ce duk da cewa jakan Najeriya na da yawa, amma da wannan adadin da ake yankawa za a wayi gari babu jaki ko daya a kasar.

Mista Pope ya ce rayuwar jakuna na da muhimmanci matuka saboda irin gudumawar da suke bayarwa wajen taya aikace-aikace musamman ma a Najeriya.

Da yawa daga cikin mutanen karkara a Najeriyar dai sun ta’allaka kan jaki a matsayin abin hawa zuwa kasuwa da zuwa gonaki har da kai iyalai asibiti a lokutan haihuwa.

More News

APC ta dakatar da Ganduje a matakin gunduma

Mambobin jam'iyyar APC a mazabar da ke Karamar Hukumar Dawakin Tofa a Jihar Kano sun dakatar da Shugaban Jam’iyyar APC na kasa Abdullahi Ganduje. ...

Wani mutumi ya kashe mahaifiyarsa a kan kudi

Jami’an rundunar ‘yan sandan jihar Osun sun kama wani mazaunin kauyen Kajola da ke kusa da Apomu a jihar mai suna Lukman Adejoju bisa...

Mayaƙan Boko Haram Biyu Sun Miƙa Kansu Ga Sojoji

Rundunar dakarun soja ta ƙasa da ƙasa wato Multi National Task Force(MNJTF) a turance shiya ta 3 dake Monguno a Najeriya ta bayar da...

Sojoji a birnin Ibadan  sun kama Æ´an fafutukar kafa Æ™asar Oduduwa

Dakarun rundunar sojan Najeriya  sun samu nasarar kama wasu mutane masu fafutukar kafa ƙasar Oduduwa a birnin Ibadan na jihar Oyo. Masu fafutukar sanye da...