Janet Jackson da Chris Brown da 50 Cent sun cashe a Saudiyya | BBC Hausa

Janet Jackson na cashewa a Saudiyya

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Fitattun mawaka da makadan Amurka sun cashe a birnin Jeddah na Saudiya, bikin casu da ‘yan kasar suka dade suna jira.

An gudanar da gagarumin bikin casun ne a dandalin Sarki Abdallah a birnin Jedda, kuma Daga cikin mawakan da suka cashe sun hada da Janet Jackson, 50 Cent da Chris Brown.

Wannan shi ne bikin casu na farko da aka taba gudanarwa a kasar Saudiyya.

Dandazon ‘yan kallo sun yi ta shewa cikin annashawa da yanayin nan na ba sa ban ba, saboda shekaru biyu da suka gabata idan aka ce za su samu dama irin haka ba za su amince ba.

baya ga Fitattun mawakan Amurka an kuma gayyato fitattun mawakan larabawa kamar Tamir Husny da Muhammad Abdou da sauransu.

Hotunan da aka yada a kafafen sadarwa na Intanet sun nuna Janet Jackson da tawagarta sun yi shiga ba kamar yadda aka saba gani ba ta tsaraici dukkaninsu sanye da bakin tufafi.

An yi casun ne ba tare da Nicky Minaj ba, wacce ta sauya ra’ayi bayan gayyatarta saboda damuwa da ‘yancin mata da masu luwadi da madigo a Saudiyya.

Ko da yake jaridar Okaz ta gwamnatin kasar ta ce ba Nicky ce ta janye bisa radin kan ta ba masarautar Saudiyya ce ta sanya ta hakan saboda yadda ake ta sukar lamirinta.

A baya-bayan nan dai kasashe daban-daban sun matsawa Saudiyya lamba kan batun take hakkin dan adam da ‘yancin fadar albarkacin baki.

Wannan ya biyo bayan kisan dan jarida kuma dan kasar Jamal Khashoggi wanda ya yi kaurin suna wajen sukar masarautar kasar da Yarima mai jiran gado Muhammad bin Salman al-Saud.

More News

EFCC na neman Yahaya Bello ruwa a jallo

Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati (Economic and Financial Crimes Commission) ta bayyana tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello a matsayin...

Mutane da dama sun mutu bayan motar fasinja ta taka bam a Borno

Akalla mutane 16 ne ake fargabar sun mutu yayin da wasu 20 suka jikkata bayan wata motar fasinja da ke kan titin Baga-Kukawa a...

Sojoji Sun Ceto Lydia Simon ĆŠaya Daga Cikin Ćłan Matan Chibok

Dakarun sojan Najeriya dake aiki da rundunar samar da tsaro ta Operation Desert Sanity III sun samu nasarar ceto, Lydia Simon É—aya daga cikin...

Gwamna da ƴansanda sun daƙile yunkurin EFCC na kama Yahaya Bello

A ranar Laraba ne Gwamnan Jihar Kogi, Usman Ododo, ya dakile wani yunkurin da Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati ta...