Jam’iyar PDP ta dakatar da Dino Melaye

Jam’iyar PDP a jihar Kogi ta dakatar da Dino Melaye tsohon ɗantakarar gwamna a jihar kan zargin cin amanar jam’iya.

Shugabannin jam’iyar PDP na mazaɓar Ayetoro Gbede 1 dake ƙaramar hukumar Ijumu ne suka dakatar da Melaye.

A wata takarda mai ɗauke da kwanan watan 12 ga watan Satumba shugabannin mazaɓar sun yi iƙirarin cewa an gayyaci Melaye kan ya bayyana a gaban kwamitin ladabtarwa a cikin watan Agusta kan zargin da ake masa na aikata ba dai-dai ba amma yaƙi amsa gayyatar.

Shugabannin sun ce ƙin amsa gayyatar da ya yi ya saɓa da kundin tsarin mulkin jam’iyar ta PDP da kuma tanade-tanaden ladabtarwar jam’iyar.

Hakan da ya yi ya zubarwa da jam’iyar mutunci saboda haka cigaba da kansacewarsa a jam’iyar ba abu ne mai yiyuwa ba.

More from this stream

Recomended