Jam’iyar PDP a jihar Kogi ta dakatar da Dino Melaye tsohon É—antakarar gwamna a jihar kan zargin cin amanar jam’iya.
Shugabannin jam’iyar PDP na mazaÉ“ar Ayetoro Gbede 1 dake Æ™aramar hukumar Ijumu ne suka dakatar da Melaye.
A wata takarda mai ɗauke da kwanan watan 12 ga watan Satumba shugabannin mazaɓar sun yi iƙirarin cewa an gayyaci Melaye kan ya bayyana a gaban kwamitin ladabtarwa a cikin watan Agusta kan zargin da ake masa na aikata ba dai-dai ba amma yaƙi amsa gayyatar.
Shugabannin sun ce Æ™in amsa gayyatar da ya yi ya saÉ“a da kundin tsarin mulkin jam’iyar ta PDP da kuma tanade-tanaden ladabtarwar jam’iyar.
Hakan da ya yi ya zubarwa da jam’iyar mutunci saboda haka cigaba da kansacewarsa a jam’iyar ba abu ne mai yiyuwa ba.