Jam’iyar PDP a jihar Benue ta dakatar da Ortom da wasu mutane uku

Shugaban jam’iyar PDP na jihar Benue, Sir John Ngebde  ya sanar da dakatar  da tsohon gwamnan jihar, Samuel Ortom  da wasu mutane uku daga jam’iyar kan zargin cin amanar jam’iya.

Sanarwar na zuwa ne ƴan awanni kaɗan bayan da 9 cikin 13 na ƴan kwamitin zartarwar jam’iyar na jihar suka ayyana Ngebde a matsayin dakatacce.

Wani tsagin jam’iyar PDP a wata sanarwa  kakakin jam’iyar Bemgba Iortyom ya sanar da cewa   ranar Litinin, Ngebde tare da wasu mutane uku an dakatar da shi daga shugabancin jam’iyar.

Amma kuma Ngebde ya yi watsi da iƙirarin a ranar Talata a yayin da yake sakatariyar jam’iyar dake Makurdi. Ya faɗawa ƴan jaridu cewa an gudanar da  taron ɗaukacin  shugabannin jam’iyar domin amincewa da dakatarwar da aka yiwa Ortom da sauran shugabannin biyu.

Ya ce ” Kana ganina yanzu a zaune a ofis da dukkanin shugabanni amma kuma ina mutanen da kake magana akansu basa ko ina a cikin ginin nan.”

Mai bawa jam’iyar shawara kan kafafen yaɗa labarai ya ce an dakatar da Ortom kan goyon bayan da ya bawa ɗantakar gwamna na jam’iyar LP da kuma umarnin zaɓen jam’iyar APC a zaɓen shugaban ƙasa na 2023.

More from this stream

Recomended