Jam’iyar New Nigeria People Party NNPP ta lashe zaɓen dukkanin kujerun ƙananan hukumomin jihar Kano 44.
Farfesa Sani Malumfashi shugaban hukumar zabe mai zaman kanta ta jihar Kano KANSIEC shi ne ya sanar da sakamakon a babban birnin jihar.
Ya ce an gudanar da zaben cikin tsari kuma lami lafiya ba tare da rahoton samun rikici ba a ko’ina.
Zaɓen kafin a gudanar da shi an yi ta samun takun saka tsakanin jam’iyar APC da kuma hukumar zaɓen bayan da wani mamba a jam’iyar APC ya kai hukumar zaɓen jihar ƙara a gaban kotu.
A ranar 22 ne ga watan Oktoba babban kotun tarayya dake Kano ta yanke hukuncin cewa Malumfashi bai cancanci shugabancin hukumar zaɓen ba.
Alƙalin kotun mai shari’a, Simon Amobede da yake yanke hukuncin ya ce Malumfashi halastaccen ɗan jam’iyar NNPP kuma hakan ya saɓawa doka.
Sai dai a ranar Juma’a babbar kotun jihar Kano ta bawa hukumar zaɓe ta KANSIEC damar gudanar da zaɓen ƙarƙashin shugabancin Malumfashi.