Jami’an tsaro sun samu nasarar kama wani jirgin ruwa dake dauke da danyen mai a yankin Niger Delta.
Wani fefan bidiyo da jami’an tsaron suka fitar ya nuna yadda aka cinnawa jirgin wuta domin ya zama izina ga sauran barayin man.
A yan kwanakin nan dai jami’an tsaro na cigaba da samun gagarumar nasara a yakin da suke da masu fasa bututun mai.


