Rundunar sojan saman Najeriya ta ce dakarunta sun samu nasarar kama Isa Abdul mai shekaru 35 wani fitaccen mai garkuwa da mutane a garin Durɓunde dake karamar hukumar Takai.
A wata sanarwa ranar Talata, Edward Gabkwet mai magana da yawun rundunar ya ce an kama mutumin tare da yaransa ranar Litinin da ƙarfe 06:30 na yamma biyo bayan ƙwararan bayanan sirri da rundunar ta samu.
Gabkwet ya ce gungun masu garkuwar su ne ke da hannu a yin garkuwa da mutane da dama a yankin.
Ya ƙarawa da cewa binciken farko da aka gudanar ya nuna cewa wanda aka kama shi ne ke da hannu wajen yin garkuwa da wani da ake kira Yakubu Ibrahim Tagaho wanda aka fi sani da Sarkin Gaya a ranar 6 ga watan Afrilun shekarar 2023 a ƙauyen Tagaho dake karamar hukumar Takai.
Gabkwet ya ce an saki Tagaho bayan wata ɗaya bayan da aka biya kuɗin fansar miliyan 30.
Har ila a cikin watan Disamba sun samu nasarar yin garkuwa da wasu yan mata ƴan uwan juna su biyu kuma sai da aka biya maƙudan kuɗaɗe kafin su sako su.