Kungiyar ISWAP mai da’awar jihadi ta kashe mutane 23 da suka hada da manoma da masunta a kauyen Malam Karanti, wanda ke da nisan kilomita biyar daga garin Baga a karamar hukumar Kukawa ta jihar Borno. Rahotanni sun bayyana cewa harin ya auku da safiyar ranar Alhamis.
Wata majiya ta bayyana cewa ‘yan ta’addan sun tattara mutane a wuri daya kafin su fara bude musu wuta, inda suka kashe 23 daga cikinsu. “Sun bar wani dattijo da rai wanda ya je ya shaida wa sauran al’umma halin da aka shiga. Yawancin wadanda aka kashe manoman wake ne,” in ji majiyar.
Bayan aukuwar harin, mazauna yankin sun yi yunkurin nemo gawarwakin wadanda aka kashe tare da hadin gwiwar jami’an tsaro, amma sai ‘yan ISWAP suka dawo suka kai wani hari wanda ya hana ci gaba da aikin ceto.
Wani mazaunin yankin ya ce, “Mun yi kokarin shiga da jami’an tsaro domin daukar gawarwakin, amma sai suka sake dawowa suka hanamu. Mutane da dama har yanzu ba su san inda ‘yan uwansu suke ba.”
Kauyen Malam Karanti dai na daga cikin wuraren da ISWAP ke amfani da su, amma mutane da dama na ci gaba da zuwa wurin don noma da kamun kifi saboda bukatun yau da kullum, duk da hadarin da ke tattare da hakan.
A halin yanzu, Babban Hafsan Tsaro na kasa, Janar Christopher Musa, ya bayyana cewa dakarun Najeriya na ci gaba da kokarin murkushe ‘yan ta’addan tare da kawar da su daga sansanoninsu.
Ya kara da cewa ana aiki kafada da kafada da kasashe kamar Rasha da Faransa don samun makaman zamani domin kawo karshen rikicin cikin lokaci. Har ila yau, ya ce ana shirin cika tafkin Chadi da ruwa domin bai wa sojoji damar shiga sassa daban-daban na yankin, musamman inda ISWAP ke fakewa domin gudanar da ta’addanci da kuma tara kayan aiki ta hanyar noma da kamun kifi.
ISWAP Ta Hallaka Manoma 23, Ta Yi Garkuwa da Wasu 18 a Borno
