‘Iran za ta yaba wa aya zaki idan ta shiga gonarmu – Amurka

John Bolton yana magana ne a taron Majalisar Dinkin Duniya na nuna adawa da Iran a New York


John Bolton yana magana ne a taron Majalisar Dinkin Duniya na nuna adawa da Iran a New York

Mai bai wa shugaban Amurka shawara kan harkokin John Bolton, ya gargadi shugabannin Iran cewa za su yaba wa aya zaki idan suka cutar da Amurka ko ‘yan kasar ko kuma kawayenta.

Maganganun nasa sun zo ne sa’o’i kadan bayan da Shugaba Donald Trump ya zargi Iran da jawo “hargitsi da mace-mace da tabargaza” a fadin Gabas ta Tsakiya.

Shugaban Iran Hassan Rouhani, ya mayar da martani ta hanyar sukar gwamnatin Trump da cewa tana cike da tashin hankali.

A baya-bayan nan Amurka ta sanya wa Iran takunkumi bayan janyewarta daga yarjejeniyar nukiliyar kasar ta shekarar 2015.

Wannan yarjejeniya wacce aka yi ta a lokacin Shugaba Barack Obama, ta sa Iran ta takaita harkokin nukiliyarta domin a saukaka mata takunkumi.

Sauran kasashen da suka sanya hannu har yanzu suna goyon bayan yarjejeniyar. Birtaniya da China da Faransa da Jamus da Rasha sun ce za su kafa sabon tsarin ci gaba da gudanar da kasuwanci da Iran tare da kuma keta takunkuman Amurka.

Sakataren Harkokin Waje na Amurka Mike Pompeo ya soki shirin a matsayin “daya daga cikin matakan da ba za su haifar da alheri ba”.

Shin me Amurka ta fadi game da Iran?

Mr Bolton ya ce “malaman addini a Tehran” masu “mulkin kashe-kashe” za su gani a kwaryarsu idan suka ci gaba da “karya da cuta da yaudara”.

Tsohon wakilin na Amurka a Majalisar Dinkin Duniya ya yi maganar ne a taron nuna adawa da Iran a birnin New York ranar Talata.

“Idan ka shiga gonarmu ko ta kawayenmu ko abokan huldarmu, ko kuma ka cutar da ‘yan kasarmu, hakika za ku yaba wa aya zaki”.

“Bari na fadi sakona dalla-dalla: Muna gani kuma za mu yi maganinku.”

Mr Bolton, wanda a can baya ya sha cewa ta hanyar daukar matakin soja ne kawai za a iya maganin Iran, ya ce Amurka ba za ta sassauta ba kan sanya takunkumin tattalin arziki.

Wanne martani Iran ta mayar?

Mista Rouhani ya ce za a fara sasantawa ne kawai idan aka daina barazana da kuma abin da ya kira “sanya takunkumin rashin adalci,” yana mai cewa babu wata al’umma da za a iya tursasa mata hawa teburin sulhu.

“Hanyar da Amurka take bi wajen yin mu’amala ta kasashen duniya ta fi kama da kama-karya. Gani suke hasashensu daidai ne.

Fahimtar da suka yi wa mulki fahimta ce da ba ta kan doka sai tursasawa da kyara,” kamar yadda ya fada a New York.

Iran ta soki Mista Trumo da cewa tana son kaddamar da yakin cacar-baka ne da ita, ta kuma yi watsi da batun cewa tana da hannu a ta’addanci.

Ta jajirce cewa shirin nukiliyarta ba na tashin hankali ba ne.

More News

Mutane 21 sun mutu a hatsarin kwale-kwale a Lagos

Fasinjoji 21 ne suka rasa rayukansu bayan da wasu jiragen ruwa suka ci karo da juna a Imore dake karamar hukumar Amuwo-Odofin ta jihar...

Mutane 21 sun mutu a hatsarin kwale-kwale a Lagos

Fasinjoji 21 ne suka rasa rayukansu bayan da wasu jiragen ruwa suka ci karo da juna a Imore dake karamar hukumar Amuwo-Odofin ta jihar...

Ma’aikatan NAFDAC a Najeriya sun fara yajin aiki

Kungiyar Manyan Ma’aikata ta Kasa da Kamfanonin Gwamnati (SSASCGOC) reshen Kungiyar Kwadago ta Hukumar Kula da Abinci da Magunguna ta Kasa (NAFDAC) ta fara...

An ƙona sakatariyar ƙananan hukumomi 2 a jihar Rivers

Wasu da ake kyautata zaton ɓatagari ne sun ƙona wani sashe na sakatariyar ƙananan hukumomin Eleme da Ikwerre dake jihar Rivers. Ƙona ginin na zuwa...