
Farashin gangar danyen man fetur ya yi sama da kaso 7 cikin dari ranar Juma’a a kasuwar duniya a karon farko cikin watanni hudu.
Farashin danyen man nau’in Brent wanda shi ne ake amfani da shi a matsayin ma’aunin farashin a kasuwar duniya ya yi sama da kaso 7.92 inda ya kama dalar Amurka 74.85 Mai makon dala 69 da aka sayar a ranar Alhamis.
Danyen mai nau’in WTI(West Texas Intermediate) ya karu da kaso 8.2 ya zuwa dalar Amurka 73.61 a karon farko tun bayan da ya kai haka a watan Janairu.
A cewar kamfanin dillancin labarai na Reuters karuwar farashin na zuwa ne bayan da Isra’ila ta kaiwa kasar Iran wasu jerin hare-hare abun da kawo fargabar cewa za a samu tsaiko kan man dake fitowa daga gabas ta tsakiya.