Inter Milan ta yi wa Lukaku tayin karshe | Sport

Lukaku

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Babban jami’in Inter Milan, Beppe Marotta ya ce ba za su kara farashi kan tayin da suka yi wa dan kwallon Manchester United, Romelu Lukaku ba.

Inter ta taya dan wasan tawagar Belgium fam miliyan 54, inda United taki sallamawa ta kuma bai wa kungiyar ta Serie A wa’adin kammala cinikin dan kwallon.

United ba ta je da Lukaku wasan sada zumunta da za ta yi ranar Talata da Kristiansund a Norway ba, bayan da bai buga wasa hudu da ta yi a Australia da Singapore da kuma China ba, sakamakon jinya.

Marotta ya ce farashin da suka yi wa Lukaku daidai yake da darajar dan wasan, ya kuma kara da cewar akwai iya kacin cinikin da za su iya yi wanda kowa zai amfana.

A ranar Litinin United ta sanar a shafinta na Intanet cewar Lukaku baya cikin ‘yan wasa 26 da za ta je da su wasan sada zumunta ranar Talata a Norway.

Mai tsaron baya ma Eric Bailly baya cikin wadanda aka bayyana da za su buga wa United wasan, har da Matteo Darmian da kuma Alexis Sachez.

Sanchez ya yi rauni ne a gasar Copa America wasan neman mataki na uku da suka kara da Argentina a farkon watan nan.

Wasan da za a yi a garin Ole Gunnar Solskjaer zai zama shirin fafatawar da United za ta yi da AC Milan a Cardiff ranar Asabar.

‘Yan wasan da United ta bayyana

De Gea da Grant da Pereira da Romero da Dalot da Jones da Lindelof da Rojo da Shaw

Smalling da Tuanzebe da Wan-Bissaka da Young da Fred da Gomes da James da Lingard da Mata

Matic da McTominay da Pereira da Pogba da Chong da Greenwood da Martial da kuma Rashford.

More News

EFCC na neman Yahaya Bello ruwa a jallo

Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati (Economic and Financial Crimes Commission) ta bayyana tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello a matsayin...

Mutane da dama sun mutu bayan motar fasinja ta taka bam a Borno

Akalla mutane 16 ne ake fargabar sun mutu yayin da wasu 20 suka jikkata bayan wata motar fasinja da ke kan titin Baga-Kukawa a...

Sojoji Sun Ceto Lydia Simon ĆŠaya Daga Cikin Ćłan Matan Chibok

Dakarun sojan Najeriya dake aiki da rundunar samar da tsaro ta Operation Desert Sanity III sun samu nasarar ceto, Lydia Simon É—aya daga cikin...

Gwamna da ƴansanda sun daƙile yunkurin EFCC na kama Yahaya Bello

A ranar Laraba ne Gwamnan Jihar Kogi, Usman Ododo, ya dakile wani yunkurin da Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati ta...