Inter Milan na son dauko Griezmann, Barcelona na zawarcin Isak

Hakkin mallakar hoto
Getty images

Image caption

Dan wasan gaban Barcelona Antoine Griezmann

Inter Milan na son karbo dan wasan Faransa Antoine Griezmann, mai shekara 29, domin ta bayar da Lautaro Martinez a wani tsari na musaya idan Barcelona ta yi yunkurin dauko dan wasan na Argentina mai shekara 22 daga gare ta. (La Gazzetta dello Sport, via Marca)

Barcelona tana son dauko dan wasan gaba na Sweden Alexander Isak, mai shekara 20, daga Real Sociedad idan bata yi nasarar sayo Martinez ba(Marca)

Dan wasan Chelsea da Faransa N’Golo Kante, mai shekara 29, na cikin jerin ‘yan wasa uku da Real Madrid za ta yi musayar su don cike gurbinsu. (AS, via Mail)

Tsohon kocin Tottenham Harry Redknapp ya ce dan wasan kungiyar Harry Kane ba zai yi katabus ba idan ya koma Manchester United ko da yake mai yiwuwa kyaftin din na Ingila “ya so komawa” ko dai Barcelona ko Real Madrid “wata rana”. (Talksport)

Za a bai wa Arsenal da Chelsea damar sayo dan wasan Barcelona Philippe Coutinho a bazarar nan, inda ake sa ran Bayern Munich za ta ki mayar da matsayin dan wasan na Brazil mai shekara 27 daga na aro zuwa na din-din-din(Sun)

Manchester United ta kalli yadda dan wasan Atletico Madrid Saul Niguez yake murza leda amma ba za ta iya biyan fiye da £70m kan dan wasan na Spaniya ba, wanda aka sanya wa farashin £132m. United na fatan jan hankalin dan wasan mai shekara 25 ta hanyar kara alawus dinsa daga £115,000 zuwa kusan £200,000 duk mako. (Sun)

Wakilin dan wasan Ajax Donny van de Beek, ya ce kungiyoyi da dama suna zawarcin dan kwallon mai shekara 22 dan kasar Netherlands, wanda ake rade radin zai koma Real Madrid ko Manchester United. (Voetbal International, via Metro)

Tsohuwar kungiyar dan wasan Manchester City Sergio Aguero, Independiente, tana kara kaimi domin dawo da dan wasan mai shekara 31 dan kasar Argentina (Mirror)

Manchester United da Real Madrid ba za su damar sayo dan wasan Borussia Dortmund da Norway Erling Braut Haaland a kan £65m ba a bazara domin kuwa sai 2022 za a sanya shi a kasuwa (Mirror)

Dan wasan Italiya Lorenzo Insigne, mai shekara 28, na shirin tsawaita kwangilarsa a Napoli zuwa 2025. (Calciomercato)

More News

Majalisar dokokin jihar Kaduna ta nemi ma’aikatar kudin jihar ta miÆ™ata bayanan bashin da El-Rufai ya ciwo

Majalisar dokokin jihar Kaduna ta nemi ma'aikatar kudi ta jihar da ta miƙa mata cikakken bayani kan basukan  da gwamnatin tsohon gwamnan jihar, Nasiru...

An dakatar da ayyukan kamfanin jiragen sama na Dana Air

Festus Keyamo, ministan harkokin sufurin jiragen sama ya umarci hukumar FAAN dake lura da sufurin jiragen sama a Najeriya ta dakatar da ayyukan kamfanin...

Yahaya Bello Ya Bayyana Dalilan Da Ya Hana Shi Bayyana A Gaban Kotu

Tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello ya ce tsoron kamun  hukumar EFCC dake yaÆ™i da yiwa tattalin arzikin Æ™asa ne ya hana shi bayyana...

Ƴan sanda sun kama mutane biyu dake samarwa ƴan fashin daji makamai a jihar Kaduna

Rundunar Æ´an sandan jihar Kaduna ta ce tana tsare da wasu mutane biyu da ake zargi da safarar bindiga a jihar. A wata sanarwa ranar...