Connect with us

Hausa

Illar sakin fursunoni daga gidajen yari kan tsaro a Najeriya

Published

on

Ko a watan Oktoban 2019 an kai hari gidan yarin Koton-Karfe da ke jihar Kogin, inda fursunoni 153 suka gudu

Ko a watan Oktoban 2019 an kai hari gidan yarin Koton-Karfe da ke jihar Kogin, inda fursunoni 153 suka gudu

Shugaban hukumar kula da gidajen yari a Najeriya Halliru Nababa ya ba da umurnin fara bincike kan yadda aka kai hari tare da balla gidan yarin Kabba a jihar Kogi da ke yankin arewa ta tsakiya.

Lamarin na ranar Lahadi da daddare ya yi sanadiyyar tserewar fursunoni 240.

Sanarwar da hukumar ta fitar ta ce Mr Nababa ya kuma umurci lalubo wadanda suka gudun a duk inda suka shiga.

Kamar yadda rahotanni suka nuna maharan sun isa gidan yarin da misalin karfe 11:45 na daren Lahadi dauke da muggan makamai, kuma ba tare da bata lokaci ba suka fara musayar wuta da jami’an tsaro.

Rahotanni sun tabbatar da kashe jami’an tsaro biyu, inda kuma ake kan neman wasu biyu a halin da ake ciki.

Sai dai gwamnan jihar ta Kogi Yahaya Bello ya ce da dama daga cikin fursunonin da suka gudu daga gidan yarin na Kabba an kama su, yayin da wasu suka dawo da kansu.

Rahotanni sun ce mafi yawan fursunonin gidan yarin Kabba din ana zargin mayakan Boko Haram be, amma hukumomi sun ce har yanzu ba su san wanda ya kai harin na ranar Lahadi ba.

Mene ne hadarin balle gidajen yari a halin da Najeriya ke ciki?

Masu sharhi kan lamarin tsaro a Najeriya sun sha bayyana irin hadarin da ke tattare da yi wa dabi’ar fasa gidajen yari rikon sakainar kashi, musamman a halin rashin tsaro da kasar ke ciki.

Lura da cewa Najeriya na cikin halin rashin tsaro a kusan duka yankunan kasar, masana na ganin idan aka yi sake, balle gidajen yari zai iya samar da karuwar ‘yan ta’adda a kasar.

A cewar Abdullahi Yelwa, malami a sashen nazarin muggan dabi’u da dakile yaduwarsu na Kwalejin Kimiyya da Kere-Kere da ke Tatari-Ali da ke Bauchi, ya zama dole a dauki matakan gaggawa kafin lamarin ya fi karfin hukumomi.

A ta bakin masanin ”karancin jami’an tsaro da kuma jinkirin yankewa tare da zartar da hukunci na daga cikin manyan abubuwan da ke rura wutar kai hare-hare a gidajen yari”.

”Abin takaici shi ne sai ka ga akwai wadanda an dade da yanke musu hukuncin kisa amma ba za a aiwatar ba sai a ajiye su a gidajen yari”.

”Kuma kasancewar su mutane masu hadari a cikin al’umma, ba abin mamaki ba ne su hada kai da yan uwansu a waje su balla gidajen yarin don fito da su”.

”Akwai kuma rashin kyakkyawan tsaro, wanda yana faruwa ne saboda karancin jami’an tsaro a gidajen yarin Najeriya,” in ji Abdullahi Yelwa.

Haka ma masanin ya ce jami’an tsaron ba su da horon da ya dace, ga kuma karancin makamai na zamani da za su iya amfani da su wurin dakile faruwar irin wadannan hare-hare.

A kan haka ya bukaci hukumomi a Najeriya da su dauki matakan zartar da hukunci ba tare da bata lokaci ba, da kuma samar da isassun jami’an tsaro tare da ba su horon da ya dace.

Wasu masu sharhin sun hankaltar da hukumomin Najeriya cewa lura da kusancin jihar Kogin da babban birnin kasar wato Abuja, akwai fargabar wasu daga fursunonin su tsallako birnin cikin sauki.

Balle gidajen yari

A shekarun baya-bayan nan mayakan kungiyar Boko Haram sun kai hare-hare gidajen yari a garurwuwa daban-daban inda suka saki fursunoni.

A watan Afrilin 2021 ma fiye da fursunoni 1,800 ‘yan bindiga suka sake bayan wani kwanton bauna da suka kai hedikwatar ‘yan sanda a kudu maso gabashin Najeriya.

‘Yan sanda sun dora alhakin hakan kan kungiyar Ipob da ke fafutukar ballewa daga kasar.

Continue Reading
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending