Hotuna: Labarin addinin Yarsan da ba a san shi ba sosai | BBC Hausa

Yarsani Soltan

Hakkin mallakar hoto
Behnaz Hosseini

Image caption

Wurin bautar na yankin Kermanshah da ke yammacin Iran. Iddinin Yarsan ya samo asali ne tun karni na 14th ko 15th Century, ya na kuma kamanceceniya da mazhabar Shi’a. Addinin na da littafi mai suna Kalam-e Saranjam, da aka dora bisa koyarwar Sultan Sahak.

Addinin Yarsan na daga cikin tsofaffin addinai a Gabas Ta Tsakiya

Ana kiran addinin Ahl-e Haqq da harshen Larabci, ma’ana mutane masu gaskiya.

An yi kiyasin akalla akwai mabiya addinin miliyan uku a kasar Iran, wadanda yawanci ke zaune a yammacin kasar inda Kurdawa ke da rinjaye. Yayin da wasu mabiya 120,000 zuwa 150,000 ke kasar Iraqi, inda aka fi kiran su da suna Kaka’i.

Wata mai bincike mai suna Behnaz Hosseini, daga jami’ar Oxford wadda ke nazari kan tsirarun addinai a kasashen Iran da Iraqi, a kwanakin baya, ta shafe lokaci mai tsaho cikin mabiya addinin Yarsani a lokacin azumin kwana uku da suke yi.

Yarsani tanbur

Hakkin mallakar hoto
Behnaz Hosseini

Image caption

Mabiya addinin Yarsani su na amfani da goge a lokutan bukukuwan addini da suke kira”tanbur” da rera wasu baitoci da kalamai da ake kira “kalam”

Yarsani Jamkhaneh

Hakkin mallakar hoto
Behnaz Hosseini

Image caption

Mabiya addinin Yarsani na taruwa a kowanne wata a wani wuri da ake kira “jamkhaneh”. Ana kiran taron da “jam”.Duk wanda ya shiga zaman na jamkhaneh dole ne ya bi wasu ka’idoji, ciki har da sanya wata hula ta musamman. Sannan su na yin da’ira su na kallon wani wuri na musamman da aka kebe a cikin jamkhaneh

Yarsani Khavankar

Hakkin mallakar hoto
Behnaz Hosseini

Image caption

Yarsani su na yin azumi uku a watan Aban na jerin watannin da kasar Iran ke amfani da su, wanda ya ke farawa daga watan Oktoba zuwa Nuwamba.

Yarsani Khavankar

Hakkin mallakar hoto
Behnaz Hosseini

Image caption

A kowanne dare, al’ummomin da ke bin addinin Yarsani su na gudanar da zaman addu’ar jam’i a lokacin azumi da suke shan ruwa idan rana ta fadi

Yarsani vow

Hakkin mallakar hoto
Behnaz Hosseini

Image caption

Ana gasa biredi da tafasasshen ruwan nama ko farfesu a lokacin shan ruwa

Yarsani pomegranate

Hakkin mallakar hoto
Behnaz Hossein

Image caption

‘Ya’yan itatuwa na ruman na daya daga cikin kayan marmari masu muhimmanci ga mabiya addinin Yarsani musamman lokacin bukukuwa

Yarsani moustache

Hakkin mallakar hoto
Behnaz Hosseini

Image caption

Gashin baki wata alama ce ta daukaka da girmamawa ga al’umar Yarsani, maza na tara gashin baki ba tare da askewa ko ragewa ba

Yarsani Jam ceremony in Iran

Hakkin mallakar hoto
Behnaz Hosseini

Image caption

Sai dai kundin tsarin mulkin Iran bai amince da mabiya Yarsani marasa rinjaye ba kamar mabiya addinin kirista da Yahudawa ko Zoroastrians. A maimakon haka, gwamnati kan dauki ‘yan Yarsani a matsayin mabiya mazhabar Shi’a da ke bin tafarkin Sufaye. Wasu daga cikin malaman Shi’a a Iran na kallon wadannan mutane da wadanda ba su yi imani da mazhabarsu ba

Yarsani Tirikardan

Hakkin mallakar hoto
Behnaz Hosseini

Image caption

Yawancin mutanen sun shaida wa Majalisar Dinkin Duniya shekarar 2018 sun gagara yi wa ‘ya’yansu rijistar haihuwa, saboda an haramta musu yin haka ba sa iya zaman makoki idan dayansu ya mutu kamar yadda addini ya tanada, sannan ba a ba su damar wallafa littafan addininsu ba , sannan ana hukunta su da cin zarafin addinin musulunci da kalaman batanci ga Annabi Muhammad SAW. Yayin da sojoji ke tilastawa wasu yanke gashin bakinsu

Wadannan hotunan mallakar Behnaz Hosseini ne.

More News

MTN yana ƙoƙarin ƙara kuɗin kati da data a Najeriya

Katafaren kamfanin sadarwa na MTN na kokarin kara kudin katin waya da na data a Najeriya. Kamfanin sadarwa mafi girma a nahiyar Afirka ya ba...

Gwamnatin Kano Ta Rage ₦500,000 A Kuɗin Aikin Hajjin Bana

Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya sanar da yiwa maniyatan Aikin Hajji da suka fito daga jihar kyautar ₦500,000 domin su cika kuɗin...

Ƴan bindiga sun sace wani limami a jihar Kogi

Ƴan bindiga sun yi garkuwa da Quasim Musa babban limamin garin Iyara dake ƙaramar hukumar Ijumu ta jihar Kogi. Lamarin ya faru ne a ranar...

Delta: An dawo da gawarwakin sojojin da aka kashe Abuja don yi musu jana’iza

Gawarwakin sojojin da aka kashe a jihar Delta kwanan nan sun isa maƙabartar sojoji ta kasa da ke Abuja. Gawarwakin sun iso ne da misalin...